Shugaba Kabila ya kafa sabuwar gwamnati | Labarai | DW | 09.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Kabila ya kafa sabuwar gwamnati

A Jamhuriyar Demukaradiyyar Kwango, Shugaba Kabila ya gabatar da sabuwar majalisar ministocin gwamnatinsa wata daya bayan nada Bruno Tsibala wani dan tawayen babbar jam'iyyar adawa ta UDPS a mukamin Firaminista.

A Jamhuriyar Demukradiyyar Kwango, Shugaba Joseph Kabila ya bayyana sabuwar majalisar ministocin gwamnatinsa wata daya bayan nada Bruno Tsibala wani dan tawayen babbar jam'iyyar adawa ta UDPS ta marigayi Etienne Tshisekedi kan mukamin Firaminista. Sabuwar majalisar ministocin ta kunshi mambobi 60 da suka hada da illahirin mambobin tsohuwar gwamnatin a yayin da 'yan tawayen jam'iyyar adawar ta UDPS suka samu kujeru hudu. 

Babban aikin da ke a gaban sabuwar gwamnatin shi ne na shirya zaben shugaban kasa da zai maye gurbin Shugaba Kabila wanda wa'adin mulkinsa ya kawo karshe nan zuwa karshen wannan shekara ta 201,7 kamar dai yadda yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar da aka cimma a ranar 31 ga watan Disambar shekarar bara ta tanada. 

Tun tashin farko dai babbar jam'iyyar adawar kasar ta UDPS ta yi fatali da matakin nadin Firaministan wanda ta ce ya saba wa yarjejeniyar ta 31 ga watan Disambar shekara ta 2016.