Shugaba Francois Hollande zai ƙara ƙwarin gwiwa ga sojojin Faransa a Mali | Labarai | DW | 02.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Francois Hollande zai ƙara ƙwarin gwiwa ga sojojin Faransa a Mali

A ziyarar' da ya ke shirin kai wa a Mali ´a ,makonnin na ukku a faɗan da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin dakarun ƙawancce da na masu kishin addini

Nan gaba a yau a aka shirya shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande zai kai ziyara a ƙasar Mali.Da farko dai shugaban zai isa a garin Sevare inda shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya na Mali Dioncounda Traore zai tarbe shi .kafin daga bisani su isa a garin Timbuktu mai daɗanɗan tarihi da ke a yankin arewancin ƙasar.

Inda aka shirya zai gana da sojojin Faransa da na Mali sannan ya ziyarci gidan addana kayan tarihi da masu kishin addinin suka ƙona,ana sa ran shugaban Francois Hollande zai yi kira ga ƙasashen Afirka da su ƙara ba da hima wajan kawo ɗauki.bayan makonnin ukku na faɗan da ake yi wanda a kan sa dakarun Faransa suka sake ƙwacce kusan dukanin yankunan da yan ta'adar suka mammaye sannan kuma ana sa ran wata ƙila zai tattauna batun maye gurbin dakarun Faransa da na Afirka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita :Usman Shehu Usman