Shugaba Bush ya yi marhabin da jawabin Nuri al-Maliki | Labarai | DW | 17.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bush ya yi marhabin da jawabin Nuri al-Maliki

Amirka ta yi maraba da matakin da FM Iraqi Nuri al-Maliki ya dauka na bude kofofin rundunar kasar ga tsofaffin jami´an sojin na zamanin tsohon shugaban kasa Saddam Hussein. Fadar White House ta yaba da jawabin da Maliki yayi inda a cikin ya yi kira ga ´yan Sunni da su koma cikin rundunar sojin kasar ta Iraqi. A kuma halin da ake ciki shugaban Amirka GWB ya ce yana shirin bayyana shirin sa na yiwa manufofin sa game da Iraqi kwaskwarima a farkon sabuwar shekara. Ya ce zai duba dukkan hanyoyin soji da na diplomasiya game da wannan batu.