1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Joe Biden: Amirka za ta gyara alaka da kasashen ketare

January 20, 2021

Shugaban Amirka Joe Biden da aka rantsar bada jimawa ba, ya ce mulkinsa nasara ce ga dimukuradiyya ta kasar ba wai ga kashin kansa ba.

https://p.dw.com/p/3oCJ0
USA Washington | Amtseinführung: Joe Biden
Hoto: Patrick Semasky/REUTERS

Mr. Biden ya ce a yanzu da ya kama aiki zai dauki matakan gyara alaka tsakanin kasar da kasashen ketaren da Tsohon Shugaban Amirka Donald Trump ya bata da su.

 Mr. Biden da aka rantsar da shi a tare da mataimakiyarsa Kamala Harris ya yi alkawarin yi wa 'yan kasar ta Amirka gabadaya adalci.


''Ina son wadanda ba su zabe mu ba, su san cewa banbancin ra'ayi bai kamata ya kai ga rarrabuwar kawuna ba. Na yi muku alkawarin zama shugaba ga gabadaya mutanen Amirka kuma zan yi wa wadanda ba su zabe ni ba adalci kamar wadanda suka zabe ni.'' inji Shugaba Biden.


Sabon shugaban na Amirka ya kuma ce hakkin duk wani dan kasa musamman shugabannin siyasa shi ne tsare gaskiya da kuma watsi da karerayi a dukkanin al'amura na yau da kulum.