Shirye-shiryen zaben shugaban kasa a Ghana | Siyasa | DW | 06.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirye-shiryen zaben shugaban kasa a Ghana

A nahiyar Afrika,Ghana ce kasa daya tillo da ta yi fuce gurin shirya zabubuka mafi tsbata. Abun da ke daya daga cikin dalillan da suka sa Obama ya kai ziyara a kasar.

Ana kwatanta kasar Ghana a matsayin kasa dake kan gaba wajen bin tafarkin demokradiyya da ma kwanciyar hankali a Nahiyar Afrika dangane da kwazo da himma, game da kwatanta gaskiya da take aiki da shi wajen ganin cewar demokradiya ta samu karbuwa a kasar. Tun sanda kasar ta fara bin tsarin demokradiyya a shekara 1992 dai ta gudanar da zabuka biyar, ko da shike ta fuskanci wasu kalubale da dama, amma dai bata yi kasa a gwiwa ba domin kuwa ta cigaba da samar da dawamamiyar zaman lafiya a sassa daban daban na kasar.

Ghana Wahlkampf John Mahama

Shugaba John Mahama

Duba yadda aka tafiyar da yakin neman zabe ya zuwa wannan lokacin ko shakka babu wannan zaben dake tafe kasa da saoi 24, za'a gudanar dashi bisa darussan da kasar ta koya a zabukan da suka gabata da ma wadanda aka gudanar a wasu kasashen duniya ta hanyar rungumar tsarin yin anfani da na'urar Computer.
A ranar talatar da ta gabata dai hukumar zabe ta shirya wa maaikatar tsaron kasar zabe na musamman dayake sune za su kula da tabbatar da cewar an samar da kwanciyar hankali a duk runfunar zaben kasar.
Halin Dattako da kwanciyar hankali a yayin zaben ya baiwa kasar daraja a duniya.

A gurin zaben, an fuskanci kalubale da dama kama daga tafiyar hawainiya da naurar keyi da rashin ganin sunayen wasu jamian tsaro a cikin rejista da dai sauransu, hakan dai ya sa jami'in hulda da jama'a na hukumar zabe mai zaman kanta Sylvia Annor ta yiwa jama'a bayani game da dalilin afkuwar haka:

Opposition presidential candidate Nana Akufo-Addo, center, looks on from the stage during his final campaign rally ahead of Friday's presidential election, in Accra, Ghana, Wednesday, Dec. 5, 2012. Far right is former Ghana President John Agyekum Kufuor. After five coups and decades of stagnation, the West African nation of 25 million is now a pacesetter for the continent's efforts to become democratic. Ghanaians will go to the polls on Friday to choose between four candidates, including President John Dramani Mahama, a former vice president who assumed the top post in July after the death of president John Atta Mills, and former foreign minister Akufo-Addo who lost the presidency by less than 1 percent in 2008.(Foto:Christian Thompson/AP/dapd)

Dan takarar NPP Nana Akufo-Addo

Tace wasu yan tsaron da ba gano sunayensu a rufunan zaben da suka je kada kuria ba, ba daga nan ne suka rubuta sunayensu tun da farko ba. Misali wani da ya rubuta sunansa a jihar yamma, sai ga shi a osu dake jihar greater Accra wai zai kada kuria, ai hakan ba zai yiwu ba kuma ba taba yin haka ba sai da izini.
Duk da hakan dai shugaban hukumar zabe mai zaman kanta yace – hukumar - a shirye take da ta gudanar da wannnan zaben cikin kwanciyar hankali tare kuma da wanke kanta daga zargin da jamaa keyi cewar za ta iya tabka magudi:

"A shirye muke mu gudanar da wannan zabe kuma zabe na musamman da muka shirya na nuna cewar muna da na'urorin aiwatar da wannan aiki. ina mai tabbattar muku cewar zai yi wuya a tabka magudi a zaben nan kamar yadda wasu ke zato domin gabannin sakamakon zaben ya kai gare ni sai wakilan jam'iyyun siyasar sun amince kuma sun sanya hannu kana ni ma in sanya hannu sai in mika wa kungiya 'yan jaridu ta kasa. kenan zan zama mahaukaci idan na yiwa wannan sakamakon kwaskwarima."

A halin yanzu dai kasar na dauke da baki dabam dabam daga kasashen ketare da zasu sa ido akan wannan zaben, bayan kawo karshen yakin neman zabe a wannan Larabar.

Mawallafa: Rahmatu Abubakar/ Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin