Shirye-shiryen zaɓe a Mali | Siyasa | DW | 17.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirye-shiryen zaɓe a Mali

Nan gaba a ranar 28 ga wannan wata na Yuli za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa,a mataki na farko na sake mayar da ƙasar bisa ta farkin demokradiyya.

'Yan takara guda 28 aka yi rejista a zaɓen da ke zaman zakaran gwajin dafi ga ɗorewar demokraɗiyya biyo bayan juyin mulkin da ya kawo tsaiko ga mulkin farar hula. Coubaly Nana Sangare 'yar shekaru 58 da ke zaune a birnin Bamako ta samu takardar zaɓen kuma ta na yin alfari da ita.

Ta ce : ''Wannan takardar zaɓe na da mahimmanci a gare ni zan yin amfanin da wannan rediyon naku domin yin kira ga 'yan Mali maza da mata da su je su samu nasu takardun saboda da wannan takardar za mu nuna cewar mu 'yan ƙasa ne, kuma da ita ne za mu iya yin zaɓe, mu zaɓi shugaban da muke so.''

Nasarar buga katunan zaɓen a kan lokaci.

Informationsmaterial der Wahlkommission CENI muss noch verteilt werden *** Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 16. Juli 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali

Katunan zaɓe

Tun can da farko mutane suna da shakKu game da cewar ko zaɓen zai gudana dangane da yadda hukumar zaɓen ta ƙasar ta fito fili ta ce ba ta san ko za ta iya buga takardun zaɓen ba kafin lokacin. To amma a yau hukumar ta ce ta rarraba takardun zaɓen kusan kishi 70 cikin ɗari ga al'umma kuma mataimakin shugaban Hukumar CENI Issaga Kampo ya ce za su iya kai ma kishi 80 cikin ɗari.

Ya ce : ''Idan aka duba yadda ake rarraba takardun zaɓen yayin da ya rage kwanaki 11 zuwa 12 a kawo ƙarshen aikin za ka cewar muna kusan kishi 70 ko ma fiye da haka na katunan da muka bai wa jama'a.''

Fargaba a kan 'yan gudun hijira dangane da zaɓen.

Issaga Kampo, erster Vize-Präsident der nationalen, unabhängigen Wahlkommission (CENI) *** Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 16. Juli 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Bamako, Mali

Issaga Kampo,Muƙadashin shugaban CENI

A kwai mutane sama da dubu ɗari biyu da suka fice daga yankin arewacin suna zaune a kudanci sakamakon yaƙin da aka yi wanda ƙungiyoyi masu kishin addinin suka kwace yanki kafin daga bisani ƙungiyar 'ya tawaye ta MNLA ta karɓe shi. Kuma duk da cewar ma gwamnatin riƙon ƙwaryar ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar 'yan tawayen to amma har yanzu jama'ar da suka fice daga yankin na arewaci ba su koma ba, Kamfo ya yi tsokaci a kan haka.

Ya ce : ''Waɗannan mutanen sune ake cewa 'yan gudun hijira kuma suna da matsalolin wajen samun takardun zaɓen, domin katunan nasu sun isa a mahaifarsu inda aka yi rejistarsu ba wurin da suke ba a yanzu, don haka wanda ke a nan yankin kudancin ka ce masa sai ya je Gao ko Kidal neman takardasa ta zaɓe zai zama matsala.''

Da wannan zaɓe ana sa ran Mali za ta sake samu martaba ga idon ƙasashen duniya waɗanda suka katse bai wa ƙasar agaji tun juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin watan Maris na shekarun 2012 wanda ya kawo ƙarshen mulkin demokradiyya.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da na taron ECOWAS a kan Mali da Guinea da aka gudanar a birni Abuja na Tarrayar Najeriya wanda wakilinmu Ubale Musa ya aiko mana.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin