Shirye-shiryen babban taron kasa a Najeriya | Siyasa | DW | 07.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirye-shiryen babban taron kasa a Najeriya

Al'ummar Najeriya na mayar da martani kan sunayen mutanen da aka zaba don su halarci taron kasa na tsakiyar watan Maris. Sai dai janye sunayen wasu wakilai da aka yi na shirin shafar manufar taron da kuma sakamakonsa.

Al'ummar Najeriya sun fara maida martani kan sunayen mutanen da aka zaba don wakiltar al'ummar kasar wajen taron kasa da za a fara nan gaba a wannan watan. Da dama dai na cewar janye sunayen wasu wakilai da aka yi ka iya shafar manufar taron da sakamakon da za a samu.

Wakilan da aka zakulo domin hakartar babban taro kasa a Nijeriya sun hada da fitattun 'yan siyasa da kuma ‘yan book irin su farfesa Jibril Aminu, da Dr Junaidu Mohammed. Sai kuma masu kare hakkin jama'a irinsu Awwal Musa Rafsanjani da ma tsofafin sojoji irin su Janar Zamani Lekwot.

Sai dai sanya wasunsu ya kara sanya takadamma ga taron da za a fara a tsakiyar watan Maris. Ita dai gwamnatin Najeriyar ta yi ikirarin cewa sai da ta darje wajen zabo mutanen da ma amincewa da wadanda aka bai wa jihohi da jam'iyyun siyasa ikon mikawa kafin amincewa da su.

An mayar da wasu masu kishin kasa saniyar ware

Nigeria Abuja Nationalrat

Tsofoffin shugabannin kasa ma na da ta cewa a taron kasa na Najeriya

Amma Dr Sadeeq Umar Abubakar Umar masanin kimiyyar siyasa da ke Najeriyar na gani ba ta canza zani ba a yadda aka saba gudanar da irin wadannan tarurruka.

‘'Ko da yake yawancin daga cikin mutanen nan mun san su suna da kishin kasa da kwarewar da ta dace a Najeriya ,amma fa duk tarurruka irin wadannan da aka yi a lokutan baya su ne dai aka yio dasu. Wadansunsu ma tun shekaru hamsin da suka wuce a Najeriya dai sune ake ta taro dasu, kuma ba abinda ya canza. To ina mutanen da suka yi tsaye a kan al'ammuran alumma suke kaiwa da kawowa a kan bada shawarwari domin samun mafita ina suke? Alal misali a jihar Plateau ina irin su Mr Solomon Dalong kowa ya san abin da suka tsaya a kai, amma ba wannan gwamnati ke so ba''.

Mata sun samu wakilici a taron kasa na Najeriya

To sai dai a bayyana ta ke cewa an samu sauyi a yadda mata suka sami wakilci sosai a cikin tafiyar, domin daga wakilai uku da kowace jiha ta turu akwai mace guda daya, baya ga sauran sassan da aka tsalma matan.

Amma ga jam'iyyun siyasa musamman na ‘yan adawa na ganin tsarin bai masu dadi ba, domin baya ga rairaye sunayen fitattun ‘yan adawa irin su Buba Galadaima na jam'iyyar APC asu samu shiga cikin taron ba, duk da turo sunansa da gwamnatin jiharasa ta Yobe ta yi. Dr Yunusa Tanko shugaban majalisar ba da shawara ta jam'iyyun siyasun Najeriya yac e akwai sake.

Nigeria Oppositionspartei APC

APC ba ta muka da wakilai a taron kasa ba

‘'Wannan sunaye da aka fito da shi bai yi ba, domin idan a ce jami'yya guda daya ta shugaban kasa ita ce taf i rinjaye a kan sauran jami'yyu, ai ka ga sune zasu fitar da mutanensu su zauna a yi wannan muhawara, amma sauran jam'iyyu na adawa wajen ashirin ba su cikin wannan muharawa. saboda haka mu ba mu yarda ba d wannan jerin gwanon sunayen da aka yi . ''

Har zuwa wannan lokaci dai jam'iyyar adawa ta APC ba ta aika da sunayen mutanen da take son su wakilceta a wajen taron ba, abinda ke kara jefa tababa a kan lamarin.Tun kafin kai wa ga wannan lokaci dai kungiyoyi daban-daban sun kasance masu nuna korafi a kan tsarin da aka bi wajen zabo wakilai da suka ganin nadin da aka saba yi aka yi. Ba wai zabe bisa tsarin demokaradiyya ba.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin