Shirye-shiryen aikin hajji na bana | Labarai | DW | 21.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiryen aikin hajji na bana

Fargaban gwamnatin Saudiyya dangane da ɓarkewar cututtuka a aikin hajji na wannan shekara

Mahukuntan ƙasar sun ce suna fatan aikin hajjin bana zai gudana ba tare da an samu barkewar cututtuka ba, musamman ma dai cutar nan ta Corono Virus wadda ake ta fargabar ɓarkewarta bayan da ta hallaka mutane 49 a cikin ƙasar.Ma'aikatar kiwon lafiyar ƙasar ta Saudiyya ce ta ambata hakan a wannan Asabar ɗin inda ta ce ta ɗauki dukkannin matakan da suka kamata dangane da batun kiwon lafiya.

Tuni dai mahajjata suka fara isa ƙasar domin sauke farali inda galibinsu yanzu haka ke Madina kafin daga bisani su isa birnin Makkah domin ci gaba da aikin na hajji. Rahotanni daga ma'aikatar aikin hajjin ta Saudiyya dai na cewar a bana ana sa ran halarta mahajjata kimanin miliyan biyu daga ƙasashe daban-daban na duniya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahman Hassane