Shirin yankewa Paul Rusesabagina hukunci | Labarai | DW | 20.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin yankewa Paul Rusesabagina hukunci

A wannan Litinin ake sa ran kotu a Ruwanda za ta yankewa Paul Rusesabagina hukunci kan laifukan da ake tuhamarsa na tallafawa aiyukan ta'addanci da garkuwa da mutane.

A wannan Litinin, wata kotu a birnin Kigali na kasar Ruwanda za ta yankewa Paul Rusesabagina hukunci. Ana zargin dan shekaru 67 da haihuwa da laifuka da suka hada da taimakawa kungiyar 'yan tawayen kasar tare da yin garkuwa da kuma aikata ta'addanci.

Rusesabagina shi ne manajan wani hotel da ya ceci dubban 'yan kabilar Tusti da Hutus a lokacin rikicin kisan kare-dangin Ruwanda na shekarar 1994, lamarin da ya sa masana'antar fina-finan Amirka ta Hollywood shirya fim mai suna Hotel Rwanda kan labarin. 

Bayan nan ne, ya soma sukar salon mulkin Shugaba Paul Kagame na kasar, daga bisani aka cafke shi, a yayin da yayi yunkurin tserewa daga kasar a watan Augustan bara, ana ganin za a iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa a hukuncin na wannan Litinin.