Shirin yajin aikin gama gari a Italiya | Labarai | DW | 11.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin yajin aikin gama gari a Italiya

Hukumomin kasar Italiya na shirin fuskantar wani babban yajin aikin gama gari na da manyan kungiyoyin kwadagon kasar suka kira a wannan Juma'a a fadin kasar.

Kungiyoyin kwadagon sun kira yajin aikin ne na awowi takwas, a wani mataki na nuna adawarsu ga matakin da gwamnatin Matteo Renzi ya dauka kan siyasar tattalin arzikin kasar. Wannan yajin aikin dai zai shafi bengarori na gwamnati da ma na masu zaman kansu, inda babban makasudin shi ne na batun kawo canje-canje ga batun samar da ayyuka da gwamnatin kasar ta sa ma gaba, inda dokar da aka rattabawa hannu a makon da ya gabata ke bada cikakar dama ga rage ma'aikata, tare da rage musu incin kariya musamman ma ga wadanda suke cikin shekararsu ta farko ta kama aiki, sannan batu na biyu da kungiyoyin kwadagon suka sa a gaba shi ne na kasafin kudin kasar na 2015, inda suke ganin matakan da aka dauka na farfado da tattalin arzikin kasar basu gamsar da su ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdou