Shirin tsige Shugaba Maduro na Banizuwela | Labarai | DW | 02.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin tsige Shugaba Maduro na Banizuwela

Hukumar zaben kasar Banizuwela ta ba da na'am dinta game da matakin farko na neman shirya zaben raba gardama da nufin tsige Shugaba Nicolas Maduro daga kan kujerar mulki.

Hukumar zaben ta amince da wannan bukata ta 'yan adawar kasar bayan da ta tattara shidar sanya hannu na 'yan kasarsu kusan miliyan biyu da ke bukatar ganin an shirya wannan zaben raba gardama a wannan kasa wacce a halin yanzu ke fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni.

Sai dai kuma duk da amincewar da hukumar zaben kasar ta yi da wannan mataki, masu adawa da akidar Chavisanci na da sauran shingayen ketara a gabansu, kafin su iya kai wa ga cimma wannan buri nasu, domin har kawo yanzu hukumar zaben ba ta bayyana ranar da za a soma aikin tattarar sanya hannu na mutane miliyan hudu wanda shi ne tsani na karshe da doka ta tanada kafin ta kira zuwa ga shirya zaben raba gardamar da zai kai ga tsige Shugaba Maduro daga kan kujerar tasa ta Mulki.