Shirin samar da ilimi ga matasa a Jamus | Zamantakewa | DW | 07.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shirin samar da ilimi ga matasa a Jamus

Hukumar kula da musayar dalibai wato DAAD ta Jamus ta tura matasa 200 zuwa sassa daban-daban na duniya domin su shafe shekara guda suna karatu.

Hukumar na yin wannan yunƙuri ne don mutunta shirin da ministocin ilimi na ƙasashen Turai suka kafa shekaru 14 da suka gabata, wanda ya tanadi bai wa daliban damar ci gaba da karatu.

Maximiliane Hurnaus, ɗaya ce daga cikin dalibai 700 da ke karantar kimiyar zane-zane da gine-ginen gidaje a jami'ar Munich da ke kudancin Jamus. Kaman sauran takwarorinta dalibai ta shafe shekara guda ta na karatu a wata ƙasa ta ƙetare, hasali ma dai a jami'ar Singapour.

Ta ce "Na Zaɓi karantar kimiyar zane-zane da gine-ginen gidaje ne saboda damar yin karatu na shekara guda a ƙetare da ake da shi. Na kwana da sanin cewar ba abu ne da zai yiwu ba idan da ni ne zan ɗauki nauyin kai na, saboda haka ban yi wata wata ba wajen ɗaukan daman da na samu hannu biy-biyu. Wannan wata dama ce ta fahimtar banbancin tsarin karatu da al'adu da ke tsakanin ƙasashen biyu. Ina ganin cewa ya kwadaitarmin da sha'awar ci-gaba da karatu."

Zumuɗin dalibai na zuwa neman ilimin

A halin yanzu dai, dalibai 180 da ke karantar kimiyar zane-zane da gine-ginen gidaje wato Architurture a jam'iyar Munich ne aka yi musayarsu a ƙasashen ƙetare. Daga cikin kudin da aka ba su har da wan´da za su iya amfani da shi wajen koyan harshen ƙasar da za su shafe shekara guda suna karatu a cikinta. Daya daga cikin waɗanda ci wannan gajiya shi ne Dominik Buhr wanda ya shafe shekarar da ta gabta ne a jami'ar Queensland na Brisbane din Australiya. Ya ce sai an je inda kayayyakin bukatun yau da kullum ke da tsada, ake sanin amfanin wannan kudi.

Manufofin hukumar ta Jamus ga daliban

Ita dai hukumar da ke kula da musayar ɗaliban Jamus ta na bayar da guraben karatu a ƙetare ne, domin bai wa matasa damar yin cudeni in cudeka da sauran takwarorinsu, tare da ba su damar ganin yadda suke gudanar da na su aiki da kuma karatu. Ko da shi ma Frank Petzold, malamin da ke koyar da zane-zane a jam'iyar kimiya da fasaha ta Munich, sai da ya da ya zayyana al'afun musayar.

Ya ce "Abu ne mai muhimmaci ɗaliban mu su samu ƙwarewar da wasu ƙasashe ke da shi, musamman ma a ƙasashe masu tasowa, kamar na yankin Latine Amirka da Indiya ko Asiya Indiya za su ga tsarinsu na gini, wanda za su iya la'akari da shi idan suka dawo gida jamus."

Su dai daliban na jami'ar kimiya da fasaha ta Munich su na iya zaɓen daya daga cikin jami'o'i bakwai da ke nahiyi hudu na duniya domin yin musayar karatu. Waɗanda ke fara cin gajiya wannan tsarin, sune waɗanda suke jin harsuna da dama, suke kuma nuna kwazo a aji.

Mawallafi : Mouhamadou Awal Balarabe

Edita : Abdourahamane Hassane