Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za ku ji cewa jam'iya mai mulki a Jamhuriyar Nijar na kan gaba a alkalumman sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalissu da ake fitarwa.
A Jamhuriyar Nijar a karon farko tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane kuma wanda ya fafata a neman shugabancin kasar tare da Shugaba Mohamed Bazoum, ya bayyana a gaban sauran jagororin 'yan adawa.
‘Yan adawa a Nijar sun ce za su yi adawa ta ci gaban kasa ba tashin hankali ba. Tuni ma dai dan takarar hamayya a zaben bara, Mahamane Ousmane ya dauki wurinsa a majalisa.
A Jamhuriyar Nijar, an kaddamar da horon sanin makamar siyasa da karfafa dimukuradiyya da kishin kasa ga matasan jam'iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula.
Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Jamhuriyar Nijar CENI tare da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya PNUDD, sun shirya bita kan zabukan kasar da suka gabata.