Shirin sabunta kundin tsarin mulki a Banizuwela | Labarai | DW | 24.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin sabunta kundin tsarin mulki a Banizuwela

Shugaba Nicolas Maduro na Benizuwela ya tabbatar da aniyar sa ta kafa kwamitin da zai rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar wannan kuwa duk da adawar da shirin yake fuskanta daga jam'iyyun adawar kasar.

Shugaba Nicolas Maduro na Banizuwela ya tabbatar da aniyar sa ta kafa kwamitin da zai rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar wannan kuwa duk da adawar da shirin yake fuskanta daga jam'iyyun adawar kasar da ke kallon sa a matsayin wani juyin mulki. 

A jiya Talata ne shugaba Maduro ya sanya hannu kan kudirin dokar da zai kayyade sharudan zaben mambobi 540 na kwamitin rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar. Tuni kuma shugabar hukumar zaben kasar Tibisay Lucena ta bayyana cewa za a gudanar da zaben mambobin kwamiti a watan Yuli mai zuwa, da kuma zaben gwamnoni a ranar 10 ga watan Disamban wannan shekara. Mutane 55 suka rasu a cikin zanga-zangar da 'yan adawar kasar suka share watannin biyu suna gudanarwa domin neman shugaba Maduro ya yi murabus.