1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayar da masu neman mafaka Ruwanda

Binta Aliyu Zurmi
June 13, 2022

Shirin mayar da masu neman mafaka zuwa Ruwanda na shan suka, amma mahukuntan Birtaniya sun kare matakin da suka ce zai taimaka wajen rage masu shiga kasar ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/4Cd6N
England London | Demonstration vor dem Gebäude der "High Commission of Rwanda"
Hoto: Wiktor Szymanowicz/AA/picture alliance

Kotun daukaka kara a Birtaniya ta fara sauraren karar da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil 'Adama suka shigar a gabanta, a wani mataki na kalubalantar matakin mahukuntan kasar na mayar da masu neman mafaka da ke zaune a kasar zuwa Ruwanda. Shirin da wadannan gammayar kungiyyoyin suka ce ya yi hannun riga da 'yancin al'umma.

Kungiyoyin sun bukaci kotun ta dakatar da shirin da a gobe Talata jirgin farko zai tashi da wasu daga cikin masu neman mafakar zuwa Ruwanda. A cewar Birtaniya, wanann shirin na da nufin rage yawan mutane da ke kwarara kasar ta hanyoyi masu hatsari da ake amfani da kananan kwale kwale daga nahiyar Turai.

Birtaniya da Ruwandan dai sun cimma yarjejeniyar mayar da wasu da ke neman mafakar siyasar, bisa biyan gwamnatin Kigali wasu kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 148 .

Akalla Mutane 30 ne ke cikin rukunin farko da zasu bar Bitraniyar, kuma duk da cewar gwamnatin bata bayyanasu ba, kungiyoyin agaji sun ce, akwai 'yan gudun hijira daga Afganistan da Siriya cikin wadanda za a mayar Ruwandan.