1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Lafiya Jari

Yusuf Bala Nayaya MA
October 12, 2018

Shirin ya yi duba ne kan sankarar mama ko kansa wadda kwararru suka gano cewa tana yi wa mata illa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/36R2p

Cutar kansa ta mama da kan kama mata, wata cuta ce da ke illa ga mata a sassa dabam-dabam na duniya ciki kuwa har da Najeriya. A kan haka masana da kwararrun likitoci suka tashi haikan don sama wa al'umma mafita.

A baya dai ana ganin tana kama mata ne da shekarunsu na haihuwa suka haura hamsin, sai dai a wannan lokaci lamarin na sauyawa saboda ana samun mata matasa masu kananan shekaru da cutar.

A jihar Kano da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, Dakta Maimuna Abdulkareem Halliru likita a asibitin kwarraru na Muhammad Abdullahi Wase, ta zurfafa bincike kan wannan cuta da sannu a hankali ke illa ga mata a jihar ta Kano.