1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moritaniya ta samu gurbi a kofin Afirka karon farko

Mouhamadou Awal Balarabe YB
November 19, 2018

Moritaniya ta samu gurbi a gasar cin kofin kwallon Afirka a karon farko cikin tarihinta, yayin da Najeriya ta sake samun dama bayan shafe shekaru hudu ba tare da an dama da ita ba.

https://p.dw.com/p/38Vq8
Africa Cup Fußball | Südafrika vs. Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/P. Magakoe

Kungiyoyin kasashen Afirka 13 sun samu tikitin shiga gasar kwallon kafar wannan nahiya da za ta gudana a shekara mai zuwa a Kamaru, bayan da suka gudanar da wasanni na hadu na neman cancanta. Tawagogin kwallon kafa na kasahen Aljeriya da Cote d'Ivoire da Guinea Conakry da Moritaniya na sahun wadanda suka kai ma gaci a karawar da suka yi a ranar Lahadi. Hasali ma a karon farko cikin tarihi, tawagar kasar Moritaniya ta samu damar shiga kofin na Afirka bayan da ta doke Botswana da ci biyu da daya, lamarin da ya sa magoya baya kungiyar Mourabitounes fantsama kan titunan birnin Nouaktchott don nuna farin cikinsu.

Fußball Nationalmannschsaft Mauretanien
Kungiyar kwallon kafa ta Mourabitounes ta MoritaniyaHoto: Imago/C. Mahjoub

A Mali ma masu sha'awar kwallon kafa sun nuna irin wannan faran cikin kasancewa a karo na bakwai a jere kasarsu ta cancanci shiga gasar Afirka bayan da ta doke Gabon da ci daya mai ban haushi. Ita ma Yuganda da ta doke Cape Verde da ci daya mai ban haushi ta samu maki 13, lamarin da ya sata hayewa. Yayin da Moroko da ta doke Kamaru a karon farko cikin tarihin kwallon kafa ta samu tikitinta ne sakamakon rashin nasarar Malawi a gaban Comores ne ya sata samun gurbi.

Ita kuwa yaya babba a fagen tamaulan Afirka, Super Eagles ta Najeriya ta tsallake zuwa gasar bayan ta yi canjaras ci 1-1 da Bafana-Bafana ta Afirka ta Kudu a karawar da suka yi a ranar Asabar a birnin Johannesburg.

A bangaren mata kuwa, gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka ta kankama a kasar Ghana karo na 13 inda ya zuwa yanzu aka gudanar da wasanni hudu a karshen mako

A rukunin farko, 'yan matan Ghana masu masaukin baki sun lallasa takwarorinsu na Aljeriya da ci daya da neman, yayin da 'yan matan Indomitbale Lions na Kamaru suka doke 'yan Mali da ci biyu da daya.

Yanzu kuma sai mu tsallako nahiyar Turai, inda ake ci gaba da gudanar da sabon lig din kasashen na Turai. Bayan tankade da rairaya tuni aka san uku daga cikin kasashen hudu da za su haye matakin da ake yi wa lakabi da Final Four, wato rukunin fitattun kasashe da za su kece raini a Portugal daga biyar zuwa tara na watan Yuni mai zuwa. Wadannan kasashe dai sun hada da Switzerland da Potugal da Ingila. Za a san kasa ta hudu da za a jera da ita bayan kece raini tsakanin Faransa da ke rike da kofin duniya da da Holland.

ATP World Tour Finals in London | Finale Alexander Zverev vs. Novak Djokovic
Alexander Zverev ya kai bantansa a wasan karshe a LondonHoto: Action Images via Reuters

A fagen Tennis, Alexander Zverev na Jamus mai shakaru 21 da haihuwa ya yi nasarar lashe kofi mafi daraja na tarihinsa, bayan da ya doke wanda aka fi ji da shi a duniya Novak Djokovic na Sabiya da ci 6-4, 6-3 a birnin london.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani