Shirin ko ta kwana a kasar Ostareliya | Labarai | DW | 16.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin ko ta kwana a kasar Ostareliya

Kowa ya fice daga ma'aikatar harkokin wajan kasar Ostareliya da ke Canberra sakamakon wani kunshi da aka gano da ba'a yarda da shi ba a kantin cin abinci na ma'aikatar

Rahotanni daga Canberra babban birnin kasar Ostareliya na cewa, jami'an tsaro sun yi shelar kowa ya fice daga ofishin ministan harkokin wajan kasar a wannan Talatar, bayan da aka gano wani kunshi da ba'a yarda da shi ba a kantin cin abinci na wannan ma'aikata. Dama dai kasar na cikin shiri, tun bayan samaman da jami'an tsaro suka kai domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a wata mashaya da ke tsakiyar birnin Sydney na wannan kasa, bayan da wani mutun ya yi garguwa da su har na tsawon sa'oi16 abun da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyu daga cikin wadanda ak ayi garkuwar da su, sannan kuma da wanda ya yi garkuwar da su. Birnin na Canberra dai inda aka gano wannan kunshi na da nisan kilo-mita 280 daga birnin Sydney inda aka yi garkuwa da mutanen.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo