Italiya na neman kafa sabuwar gwamnati
August 21, 2019Shugaba Mattarella zai soma tattaunawa ta waya a yammacin wannan Laraba da tsohon shugaban kasar ta Italiya Giorgio Napolitano mai shekaru 94 a duniya. Bayan nan shugaba Mattarella zai gana da farko a wannan Laraba da shugabannin majalisun kasar kana da shugabannin rukunin 'yan majalisar dokokin jam'iyyu a majalisar kafin a gobe Alhamis ya karkare da rukunin 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar M5S wacce ke da rinjaye a majalisar. Sai dai tsohon Firaministan kasar Matteo Renzi na Jam'iyyar Democratic Party ya ce akwai mafita daga cikin wannan danbarwa:
"Ina ganin kafa kawance tsakanin jam'iyyar M5S da jam'iyyata ta DP na iya kasancewa mafita ga wannan matsala duk da yake cewa mun taba fuskantar sabani da su a baya, amma a yanzu makomar Italiya ita ce ke da muhimmanci"
A ranar takwas ga wanann wata na Agusta ne dai shugaban jam'iyyar masu kyamar baki Matteo Salvini ya fice daga cikin kawancen da ke mulki a wani mataki na neman sake shirya zabe a kasar da kyadayin zai samun damar lashe shi domin kafa gwamnati da za ta ba shi damar aiwatar da manufofin siyasarsa da ya kasa aiwatarwa a karkashin gwamnatin kawance ta Firaminista Giuseppe Conte.