Shirin gudanar da zabuka a Zimbabwe | Labarai | DW | 23.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin gudanar da zabuka a Zimbabwe

Zimbabwe ta ce ta shirya tsaf domin yin zaben shugaban kasa mai inganci.

Hukumomin kula da harkokin zabe a kasar Zimbabwe sun sanar - a wannan Talatar cewar, a shirye suke domin gudanar da zabuka nan mako guda da ke tafe, duk da fargabar da wasu ke yi na yiwuwar tafka magudi da kuma rashin isassun kudaden gudanar da zabukan.

Joyce Kazembe, mataimakiyar shugaban hukumar zaben kasar ta Zimbabwe, ta shaidawa masu sanya ido a kan zabe, cewar, kasar za ta gudanar da zabuka cikin 'yanci da adalci da kuma walwala, kuma a shirye suke su tabbatar da hakan. Hukumar zaben ta ce kimanin mutane miliyan shidda da dubu 400, kwatankwacin rabin al'ummar kasar ne suka cancanci jefa kuri'arsu a ranar 31 ga watan Yulin nan da muke ciki.

Za a yi fafatawar ce a tsakanin shugaban kasar da ke kan mulki Robert Mugabe da kuma babban abokin hamayyarsa, kana firayi minista Morgan Tsvangirai. Sai dai kuma tuni aka ruwaito fuskantar matsaloli daban daban a zaben da jami'an hukumomin tsaron kasar suka yi, wadanda suka hada da karancin katunan zabe da kuma rashin tawada, matsalolin da kuma suka hana dubbannin jami'ai jefa kuri'unsu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru ALiyu