1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bikin raya al'adar karatun litattafai

May 20, 2021

A watannin Afrilu da Mayun kowace shekara, matasa da yara masoya karatun litattafai na samun kwanaki biyu na musamman dan bukukuwan da ke fadakar da jama’a dangane da mahimmancin karatu. 

https://p.dw.com/p/3tgJy

Misali, a ranar biyu ga watan Afrilun bana aka yi ranar litattafan yara na duniya. Sannan ranar 19 ga watan mayu, wato larabar da ta gabata aka gudanar da ranar karatu tare, a lokaci guda a kasa baki daya. Karkashin jagorancin Hukumar da ke kula da dakunan karatun Australiya. Sannan kuma za’a watsa wannan karatu ta kai tsaye a shafukan yanar gizo-gizo. A shirin da aka yi ranar 19 ga watan Mayu, hukumar da ke kula da dakunan litattafan kasar ta hada kai da shugabanin sashen kula da kimiya da na hukumar binciken sama janati.

Bayan haka ne suka zabi littafi mai suna Space wanda daya daga cikin wadanda ke kai ziyara sararin sama ko kuma Astronaut a turance, Shannon Walker ta karanta kuma duk makarantu, da dakunan labarai da ma duk kungiyoyi na Matasa da yara da ke kasashen Australiya da New Zealand  suka saurara da misalign karfe 11 na safiya. Philip Bunting ne ya rubuta littafin na Space. Bunting ya ce sai da ya dauki kusan shekara guda yana bincike kafin ya iya rubuta littafin har ya wallafa shi. Daga cikin wadanda suka tallafa mi shi a binciken har da ma’aikatan NASA a Amirka.