Shirin bayar da ilimi kyauta a kasar Ghana | Labarai | DW | 29.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin bayar da ilimi kyauta a kasar Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya dukufa wajen ganin nan gaba 'yan kasar sun samu ilimi kyauta wanda hakan zai bada damar yaki da talauci, da kuma tsarin bunkasa kasa.

Mädchenschule in Kumbungu Ghana (DW/M. Suuk)

'Yan makaranta a kasar Ghana

Kasar Ghana ta dukufa wajen ganin nan gaba ta samar da ilimi kyauta ga dukannin 'yan kasar ko ma daga ina suka fito. Ana ganin cewa wannan tsari dai zai kawo sauyi ga rayuwar miliyoyin matasa musamman ma 'yan mata da ke da karanci a cikin makarantun kasar.

Shugaban kasar ne dai Nana Akufo-Addo ya sha alwashin yin hakan tun a lokacin yakin neman zabensa. A yanzu dai shiga makarantun sakandire a kasar ta Ghana ya wajaba ne daga cin jarabawa a matakin farko, sannan ga adadin guraben da ake bukata, sai kuma idan iyayen za su iya biyan kudadan karatun 'ya'yan su.

A watan da ya gabata dai shugaba Akufo-Addo ya kara jadda aniyarsa ta ganin an kai ga kammala wannan tsari, wanda zai bai wa 'yan kasar damar samun ilimi, da kuma bunkasar kasa. Shugaban na Ghana dai ya kara da cewa, idan har ana so a yi yaki da talauci, to dole ne sai an zagine wajen samar da ilimi ga 'yan kasar musamman ma 'yan mata da basa samun hakan a yanzu.