SiyasaAfirka
Tasirin sarka a kwalliyar matan Afirka
March 8, 2021Talla
Burin wasu ‘yan mata da manyan mata, su suyi kwalliya su yi kyau kuma a yaba da su. Sai dai ko wace mace nada irin ado da ke burgeta domin da dama daga cikinsu na amfani da sarka da zobe ko dan kunne dama jigida a matsayin abin da ke karawa kwaliyarsu kyau.
Wasu na ado ne saboda burge mazajensu ko samari ko don jin daddinsu. Wasu na yi ne saboda su burge jama'a. Sarka nada nau’i irin dabam, akwai sarkar wuya da ta hannu sai kuma ta kafa, kuma ko wace irin mace da wanda ta fi sha’awa. Shin ko ya mazan ke kallon mata masu ado da sarka musanman sarkar kafa? A saurari gundarin shirin don jin cikakken bayani.