AAI
September 16, 2019Talla
Shirin na wannan lokaci ya leka ne kasar Afghanistan, inda matan kasar ke nuna fargabar halin da za su iya kasancewa a nan gaba idan aka cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Amirka da mayakan Taliban. Tattaunawar da ake gudanar da ita kusan tsawon shekara guda a Qatar, ana yin ta ne domin nemo hanyar da sojojin Amirka za su kammala ficewa daga kasar ta Afghansitan baki daya da kuma ajiye makamai a bangaren mayakan na Taliban. Bisa shiga tsakanin na Jamus, aka fara tattaunawa a tsakanin 'yan Afghansitan din domin lalubo mafita ga makomar kasar. A lokaci guda, matan kasar na fargabar cewa cimma yarjejeniya da 'yan Taliban ka iya salwantar da 'yancin da suka samu a baya-bayan nan.