1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rayuwar mata dalibai a jami'a

Ahmed Salisu GAT
August 19, 2019

Shirin Abu Namu na wannan mako ya duba rayuwar mata dalibai a jami'o'in Nijar, kalubalan da ke tattare da ita da kuma yadda jam'a ke kallon wannan rayuwa tasu.

https://p.dw.com/p/3O7RR
Niger DW-Diskussion über Internet-Gefahren in Maradi
Hoto: DW/T. Suttor-Ba

A kasashen Afirka musamman ma a yankuna da Hausawa ke da yawa, akwai muhawara mai karfin gaske da ake yi kan yanayi na tarbiyya ta dalibai mata da ke karatu a jami'a. Wasu dai na yi musu kallon mutanen kawai yayin da su daliban mata kan ce ba haka lamarin yake ba domin galibinsu karatunsu suke yi jami'a kamar takwarorinsu maza ba wai yawon banza ne ya kai su ba. Shirin ya duba yadda lamarin yake a Jamhuriyar Nijar.