1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Toshi ko kyauta ga samari da 'yan mata

Yusuf Bala Nayaya LMJ
September 3, 2018

A shirin Abu Namu da ke duba lamuran da suka shafi mata da kananan yara, a wannan karo da ke zuwa bayan kammala bukukuwan Babbar Salla, za mu ji muhimmanci toshi ko kyauta da samari ko 'yan mata ke ba wa junansu.

https://p.dw.com/p/34DSF
ScreenshotsDW Sendung eco@africa
Hoto: DW

Sabanin lokutan baya da samari ke kokari su ga sun fita kunyar 'yan mata wajen kai musu kyaututtuka da a al'adar bahaushe ake kira toshi, yanzu dai tana neman sauya zani, inda matan ne ke daukar nauyin kyaututtukan ga maza abin da ke sa wasu mazan fasa kai da jin cewa su fa ba dama ne 'yan matansu na sonsu suna aiko musu kyaututtuka kamar naman layya. Shin ko ya abin yake?A cewar wasu matan mazan ne suka yadda nasu nauyin su kuma suka dauka. An dai kai ga mataki na korafi inda a maimakon lokutan baya tun zamanin kaka da kakanni ake ganin iyaye idan sun ga 'yar budurwa ko da ma jaririya ce sai ka ji an fara kai toshi da kyaututtuka ana cewa an yi wa saurayi wane kamu na irin matar da zai aura. Haka matasan kan tashi har akai ana ba shi kyauta ya kai wa budurwa kafin lokacin da zai tsaya da kafarsa. Sai dai a wannan lokaci al'amarin na neman juyewa inda matan ke neman karbar ragamar ba da kyaututtuka, to ko me ke jawo hakan? A fadar Aishatu Yahaya wata matashiya a jihar Bauchin Najeriya matasan ne fa na yanzu ba su da zuciya.
Kokari na gyara zaman duniya ko na daukar al'adar wasu a fadar Maryam Salihu karancin sani na al'ada da ma addini shi ya jefa matan cikin wannan hali. Sai dai yayin da Maryam ke ganin matan na neman wuce gona da iri a kokari na samun yardar samarin a soyayya, su kuwa Akibu Ahmad Baba da Abubakar Umar na da nasu ra'ayin a zantawa da Aliyu Muhammad Waziri wakilinmu a Bauchi Akibu Ahmad Baba na mai ra'ayin cewa matan ne na zamanin yau ke da yawa idan aka kwatanta da lokutan baya. To shirin na wannan lokaci ya kuma leka Jamhuriyar Nijar yankin Damagaram. Ko ya mata ke kallon batun ba da kyaututtukan ko toshi a garesu musamman a baya-bayan nan lokacin sallah? A cewar wasu matan ana samu amma ba kamar da ba wasu kuwa ba sa bayarwa sun barawa mata, mazan ma ta kansu suke sai dai mace ta bayar don saurayin ya so ta. To ko shin ya kamata a ce an bar ba da kyautika ga mata ganin raunin da suke da shi? A cewar Kabiru Alkasim Ayuba ya zama dole mazan su rinka bayar da kyautar domin karfafa dankon soyayyarsu. Shi ko Sadi malam mai Kifi jan hankali ya yi ga samarin su sake damara wajen kulawa ba da kyaututtuka ga matan mai makon jiran mata su basu don gudun halakar da su.

Bildergalerie afrikanische Kopftuchmode
Hoto: DW/T. Amadou