Shirin Abu Namu: 20.02.2019
February 25, 2019Talla
Shirin Abu Namu na wannan makon ya duba halin taskun da yara kanana ke tsintar kansu a ciki a yankunan da ake fama da rikici ko kuma yake-yake. Wani sabon rahoto da kungiyar agaji ta kasa da kasa ta "Save the Children" hadin gwiwa da cibiyar bincike kan zaman lafiya ta Oslo suka fitar ya yi nuni da cewa yawan yaran da ke zaune a yankunan da ake fama da rikici na karuwa.