1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Shin yakin basasa na dab da sake barkewa a Libya?

August 19, 2024

Tare da gwamnatoci biyu masu gaba da juna a kowane bangare na kasar, ana ci gaba da tashe-tashen hankula na siyasa, kuma, a halin yanzu, ana fargabar Libya za ta iya fuskantar karin tashin hankali da yaki.

https://p.dw.com/p/4je8Z
Hoto: Getty Images/M. Turkia

 A tsawon makon da ya gabata, hukumomi da dama na kasa da kasa sun yi jan hankali a game da Libya. A cikin wata sanarwar wata kungiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke tallafa wa gwamnatin wucin gadi a Libya ta ce ta damu kwarai kan yadda ake gangamin tara mayaka a sassa dabam-dabam na Libya.  Kungiyar ta majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da UNSMIL  wadda aikinta shi ne tallafa wa gwamnatin wucin gadi da kawar da rikice-rikice da aiwatar da yarjejeniyoyin zaman lafiya da kare hakkin dan Adam a Libya ta bukaci dukkan bangarori su kwantar da hankula su kuma nuna sanin ya kamata su kauce wa dukkan wani abu da zai tada hankali ko tsokana da za ta kai ga fada.

Libyen Kämpfe um Tripolis
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

A ranar Alhamis tawagar kungiyar tarayyar Turai zuwa Libya ta nuna irin wannan damuwa cewa amfani da karfi na iya kassara zaman lafiya a Libya da ma jawo tsananin wahala ga al'umma. Tana mai cewa a cikin wata sanarwa ya kamata a kauce wa dukkan wannan ko ta wani hali. Tsawon lokaci manazarta da ke bin yadda al'amura ke wakana a Libya sun fito karara inda suka ce bayan shekaru na kwarya-kwaryar zaman lafiya a Libya, alamu na nuna yiwuwar sake barkewar yakin basasa a kasar. Wannan gargadi ya zo sakamakon matakin da daya daga cikin bangarori masu mulki da ke adawa da juna ta dauka na tara gangamin mayaka.

Infografik The conflict in Libya EN

Tun shekarar 2014   Libya ta dare gida biyu inda gwamnatoci da ke adawa da juna daya ta ke gabashi dayar kuma a yammacin kasar. Gwamnatin da ta sami goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wadda aka fi sani da gwamnatin hadin kan kasa tana zaune a Tripoli a yammacin kasar, abokiyar hamayarta kuma tana gabashi a birnin Tobruk. A lokuta da dama cikin shekaru goma da suka wuce, kowane bangare ya yi kokarin kwace iko daga dayan amma abin ya ci tura. Gwamnatin da ke gabashin Libya tana samun tallafin tsohon madugun yaki da ya rikide ya zama dan siyasa Khalifa Haftar wanda ke jagorantar kungiyoyin 'yan bindiga a yankinsa. Hasali ma dai mayakan Haftar ne suka turfafi birnin Tripoli a makon da ya gabata. A shekarar 2019 Haftar ya kai wa birnin hari amma daga baya aka tilasta sanya hannu a kan yarjejeniyar tsagaita a 2020.

Konflikt in Libyen | Kämpfe
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Salahuddien

 Haftar ya ce mayaka da ke karkashin jagorancin dansa Saddam suna kokarin kare iyakokin Libya ne don yaki da safarar miyagun kwayoyi da fataucin dan Adam da kuma yaki da ayyukan ta'addanci. Sai dai kuma manazarta na ganin akwai wata manufa ta dabam. Emadeddin Badi, wani kwararre kan Libya, ya yi tsokaci da cewa: ''Kasashen duniya sun yi watsi da Libya wasu ma sun fara rudin kansu da tunanin abin da ba zai yi wu ba cewa wai komai zai daidaita, ko dai ta ci gaba da matsayin da ake ciki a yanzu ko kuma wata yarjejeniya da wadanda suka kama wasu yankunan kasar suka rarrabata. Sai dai kuma irin wannan tunani  ya fara gushewa sannu a hankali kuma yanzu wani sabon tashin hankali ne yake tasowa. Dalili zan iya cewa shi ne har yanzu a Libya ana da tunanin sai wani ya rasa, wani zai samu. Kuma bangarorin da ke fada da juna na jin kansu cewa yadda suka dama haka za a sha musamman saboda goyon baya ko daurin gindin da suka samu daga kasashen waje.''

Janar  Khalifa Haftar
Janar Khalifa HaftarHoto: Getty Images/AFP/A. Doma

A matakin martani na gangamin mayakan sauran kungiyoyin 'yan bindiga da suke goyon bayan gwamnatin Tripoli da ke yammaci suka kara daura damarar zama cikin shirin yaki. Kwana guda bayan da aka hangi gangamin mayakan Haftar aka yi arangama tsakanin wasu kungiyoyin 'yan bindiga a Tajoura a wajen gabar ruwan Tripoli inda aka kashe mutum tara. A wannan makon ga alama, al'amura sun lafa a Libya sai dai kuma har yanzu da sauran rina a kaba a cewar  Emadeddin Badi.