1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru uku da faɗuwar gwamnatin Mali

Abdourahamane HassaneMarch 23, 2015

Magoya bayan tsohon shugaban Mali wanda ke gudun hijira a Senegal watau Amadou Toumani Toure na buƙatar ya koma gida.

https://p.dw.com/p/1EvcY
Amadou Toumani Toure Präsident von Mali
Amadou Toumani Toure tsohon shugaban ƙasar MaliHoto: AP

Yau shekaru uku ke'nan sojoji suka kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure shugaban Mali a ƙarƙashin jagorancin Amadou Haya Sonogo a ranar 22 ga watan Maris na shekaru 2012. Juyin mulkin da ya gaggauta yin kutse na masu yin jihadi a ƙasar,kuma tun daga lokacin shugaban Mali yake yin gudun hijira a birnin Dakar na Senegal.

Magoya bayan Amadou Toumani Toure na fatan ya koma gida

Wannan ita ce fafutkar da ƙungiyoyi na magoya bayan tsohon shugaban ƙasar suke yi na ganin tsohon shugaban Amadou Toumani Toure ya koma.Nouhoum Togo shi ne sakataran kula da yaɗa labarai na ƙungiyoyin masu fafutuka.''An samu kusan watanni 18 na kwanciyar hankali saboda ƙokarin da tsohon shugaban ya bayar na ganin an samu zaman lafiya.Ta ƙaƙa wannan mutumin cikakken ɗan ƙasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya za a tilasta masa yin ritaya da ƙarfi a harkokin siyasa.''

Kämpfe in Mali Mai 2012
Hoto: dapd

Har ya zuwa yanzu 'yan Mali ba su gamsu ba da sabuwar gwamnatin.
Shekaru uku dai bayan faɗuwar gwamnatin ta ATT ,Mali ta samu sabbin hukumomi sai dai har ya zuwa yanzu abin da 'yan Mali suka jira ganin an samu na sauyi musammun ma a fannin tsaro wanda ya shafi rikicin arewacin ƙasar, ba ta canza zane ba a cewar Birama Fall wani dan jarida mai yin sharhi a kan al' amura
'' 'Yan Mali da dama sun yi nadama da lamarin kuma suna cikin bacin rai idan suka tuna da tsohon shugaban ƙasar wato ATT, wanda ya buƙaci da a gudanar da taro na ƙasa da ƙasa a kan Mali a birnin Bamako saboda tun a lokacin ya gano cewar matsalar arewacin Mali ba matsala ba ce ta ƙasar kawai.''

Yayin da wasu 'yan Mali suke neman tsohon shugaban ƙasar ya koma gida, wasu na ganin shi ne ya yi sakaci ƙasar ta faɗa cikin tashin hankali don haka ba su buƙatarsa. Kawo yanzu dai babu wani furci da hukumomin Mali suka yi a kan wannan buƙata sannan kuma shi kansa tsohon shugaban bai ce ufan ba a kan batun.

Regierungswechsel in Mali - Präsident Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban Mali mai ci a yanzu Ibrahim Boubacar Keita -Hoto: picture-alliance/dpa