Shekaru biyu da kashe Osama Bin Laden
May 2, 2013Da zaran an yi maganar Al-Qaida abu na farko da jama'a suke yin tunani a kansa shi ne hare haren 11 ga watan Satumba, wanda ƙungiyar ta kai a shekarun 2001 akan cibiyar kasuwanci ta duniya wato World Trade Center. Wanda a cikin mutane kusan dubu uku suka mutu kana wasu da dama suka jikata.
Sojojin ƙundunballa na Amurika waɗanda yawan su ya kai kusan 300 sun daɗe suna yin bincike akan iyakar Afaganistan da Pakistan domin farautar Bin Laden ,ko a mace ko a raye , wanda a ƙarshe suka kashe shi a gidansa da ke a Abottabad a Pakistan.
Ƙarfin ƙungiyar Al-Qaida ya ragu bayan mutuwar Bin Laden
Bayan mutuwar ta Bin laden dai ƙungiyar ta Al-Qaida ta samu rauni kamar yadda Guido Steinberg na wata cibiyar binciken kimiyyar siyasa a nan Jamus ya nunar a cikin wata hirar da tashar DW ta yi da shi.
Ya ce:'' Jagoran ƙungiyar na yanzu Ayman Al Zawahiri ya na daga cikin shugabannin ƙungiyar wanda ake ta yawan yin tsokaci akan su, na rashin samun amanar ya'yan ƙungiyar baki ɗaya.''
A yanzu za a iya cewar magoya bayan ƙungiyar ta Al Qaida a duniya sun kai dubu goma misali, kuma kungiyar ta yaɗu da gaggawa a cikin ƙasashe inda ta ke da rasa, da dama a cewar SteiNberg.
Ya ce :'' A kwai rasa ƙungiyar a Iraki a yankin arewacin Afirka zuwa Aljeriya, da Somaliya da Libiya da kuma Mali. Ƙungiyar ta samu ƙarin ma'abiya a Iraki inda ta ke da kimanin mutane dubu.''
Ƙasashen duniya na ƙara ɗaukar matakan yaƙi da ta'addanci
An dai kai ga samun ragowar kai hare hare na ta'addanci a duniya na ƙungiyar saboda tsattsauran matakan yaƙi da ta'addanci da ƙasashen duniya suka tanada tun bayan hare haren na 11 ga watan Satumba. wani bincike na ƙwarraru ya nuna cewar ƙungiyar ta Al Qaida ta fi kai hare hare a cikin ƙasashen musulumi kana kuma mafi yawanci waɗanda ta ke kashe wa musulumi ne. Musammun ma dangane da yadda ƙungiyar ta samu kafuwa a cikin ƙasashen larabawa irin su Siriya, da Yemen da Tunisiya. wanda masana ke ganin cewar, wata sabuwar dabbara ce, ta jahadi da ƙungiyar ta ke yi a cikin ƙasashen larabawan. Inda magoya bayan ƙungiyar ke kai hare hare na ta'addanci a cikin yankunan su, wanda lamarin ya ƙarfafa a cikin shekaru huɗu na baya baya nan.
Dukkanin al'ummomin duniya na yin Allah Wadai da ayyukan ta'addanci
Ba shakka al'ummomin duniya baki ɗaya kama da ga musulumi zuwa ma'abiya addinin krista da ma waɗanda ba su da addini, ko wanne na yin Allah Wadai da lamarin ta'addanci. Kuma ko da shi ke an karya lagon ƙungiyar ta Al -Qaida, tun bayan mutuwar Osama Bin Laden har yanzu dai a kwai buƙatar zage damtse wajan yaƙi da ta'addancin a duniya baki ɗaya.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto da kuma Rahoton da Mahammadou Awal Balarabe ya haɗa mana dangane da yaƙi da ayyukan ta'addanci da ƙasashen duniya suke yi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar