Shekaru 65 da fara safarar kaya a kwantena
A ranar 26 ga watan Aprilu 1956, jirgin ruwa ya yi dakon kaya cikin kwantena karo na farko a duniya. Kirkiro hakan da Ba'amirke mai asalin kasar Sikotlan ya yi, ya zama ginshikin bunkasa kasuwanci a duniya.
Mutum da akwatunansa
A 1956, Malcom McLean, wanda ya mallaki jirgin ruwa ya bullo da babbar dabarar dakon kaya a cikin akwatuna, maimakon dakon kayan a dai-daikunsa, wanda ya kawo saukin lokaci da aikin dakon. Kuma hakan na nufin saukin kudi wanda babbar hujja ce.
Miliyoyin akwatuna da suka dawo
McLean wata kila ya tuna kawo sauki ga ma'aikata a tashoshin jiragen ruwa bawai na Amirka kadai ba amma duniya, inda kwantenonin farko suka isa. Kirkiro da hanyar ya yi matukar taimakawa, amma kuma ya jawo rasa ayyuka a lokacin.
Zahirin katafaren jirgin ruwa
A 1956, McLean ya sayi manyan tireloli inda ya maida su kamar wannan jirgi da ku ke gani, wanda a yanzu katafaren jirgin ruwan kamfanin HMM Algeciras na koriya mallakar kamfanin jiragen ruwa na Hyundai, mai daukar kimanin ton 24,000 a lokaci guda. Jirgin mai tsawo mita 400 zurfinsa ya kai mita 16. Girmansa ya sa ba ko wace tasha ya ke iya tsayawa ba.
Kwantenonin farko sun isa Jamus
A watan Mayun 1966, tashar jiragen ruwa ta Bremen: Jirgin ruwan McLean ya kawo kwantenoni 110 na farko a kasar Jamus. A wurin ne za a iya ganin zahirin kirkirar McLeen. Nan ne aka ga nasarar aikin. Bisa sabuwar dabarar ba tare da sauke kayan a kasa ba, ake iya loda shi cikin jirgin kasa.
Ka'idar kwantena
Girman kwantenoni nau'i biyu ne: Akwai mai tsawon kafa 20 kamar wanda ake gani a hoton nan, sai kuma mai kafa 40. Kwantenoni kala-kala ne. Akwai mai sanyaya kaya, akwai na musamman don dakon dabbobi ko kuma na dakon kayayyaki.
Kullum muhimmancinsa na karuwa
Akwai kayayyaki da yawa da ake safararsu a duniya. Idan ana batun kasuwancin duniya, kashi 90 cikin dari ana safararsa ne ta jiragen ruwa. jirage na kan teku, ana lodi ana sauke kaya dare da rana, aikin ba ya tsayawa, kamar yadda ake gani a nan tashar jiragen ruwa na Hamburg, kampanin mai suna Alhpaline, ya ce wannan kwantenoni 6,220 da ke dakon kaya mai nauyin ton miliyan 24.4
Tashar jiragen ruwa da aka hada ta na jiragen kasa
Tashar jiragen ruwa na Hamburg, ana hangen na'urorin lodi da sauke kwantenoni inda suka inganta layin dogo a gabar ruwan. A takaice dai kawai suna da ta su tashar jiragen kasa wanda kan kawo ko kuma ke daukar kwantenoni da jiragen ruwa ke dakonsu.
Komai na karkashin kulawa
Girman kaya da yawan kwantenoni na bukatar tsari, kula da kiyayewa. A wannan tashar jiragen ruwan Hamburg dakin kula da jiragen ruwan tamkar irin na manyan tashoshin jiragen sama na kasa da kasa ne.
Gayyata ga masu sumoga
Kasancewar miliyoyin kwantenoni da ake safararsu kullum izuwa fadin duniya, da wuya ake iya sanin komai da ke cikinsu. Bata-gari na amfani da wannan damar iya kokarinsu. A nan Birgediya Janar Ashfaqur Rashid Khan na kasar Pakista, yana tsaye wajen muggan kwayoyi da jami'ansa masu hana ta'ammali da muggan koyoyi suka kwace a cikin jirgin ruwa.
Kwantena kan iya birgewa
Sabanin yadda ake daukar kwantena abu ne mai datti da rashin fasali. Amma idan aka jera kwantenoni sukan zama abun sha'awa bisa kalolinsu da yadda fasalinsu yake sabanin yadda ake tunani, kamar wannan hoto da aka dauka cikin dare a tashar jiragen ruwan Hamburg.