Duniya ta tuna da bajintar Armstrong
July 21, 2019Talla
An gudanar da bukuwan tunawa da shekaru 50 da bajintar Neil Armstrong da ya fara sa kafa a duniyar wata, daruruwan jama'a sun halarcin gidan tarihin sama jannati a birnin Washington na kasar Amirka domin karrama wannan rana.
Akalla mutane dubu 250 ne suka kalli lokacin da Neil Armstrong ya yi wannan muhimmiyar tafiya ta talabijin a shekarar 1969, Neil Armstrong ya mutu shekaru bakwai da suka gabata.