Shekaru 50 da sauya sunan birnin Kinshasa
Kafin shekaru 50 Léopoldville ake kiran birnin Kinshasa. Shi ne babban birnin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango wanda yake bin sahun biranen Lagos na Najeriya da Alkahira na Masar wajen yawan mazauna.
Tashin hankali da 'yanci
Jim kadan kafin samun 'yancin Kwango: Ma'aikata sun yi zanga-zanga a shekarar 1959 a birnin Léopoldville. Sun nemi ganin cikakken 'yancin Kwango daga Turawan mulkin mallaka na Beljiyam. Haka ya janyo tashin hankali da amfani da karfi. Mutane 40 sun hallaka sannan wasu 250 suka jikata. Shekara daya baya (1960) kasar ta samu 'yanci.
Motocin safa masu amfani da lantarki a Kinshasa
1955: motar safa da ake caji a wata tasha da ke birnin Léopoldville. Wannan fasaha 'yan Beljiyam masu tafiyarwa sun samo daga Switzerland. Motocin suna tafiya ta kimanin kilo-mita uku. Wannan fasaha take tashe a duniya lokacin. Zuwa shekarar 1956 wadannan motocin safa sun yi jigilar fasinjoji kimanin milyan 10.
Dan kama karya ya dauki madafun iko
Ranar 30 ga watan Nowamba 1965: Shugaba Joseph Mobutu yana zaune a majalisar dokoki a tsohon birnin Léopoldville. Babban hafsan sojojin ya yi juyin mulki kwanaki biyar ke nan inda ya tunbuke gwamnatin Joseph Kasavubu shugaba na farko. Shekara daya bayan haka aka sauya sunan birnin zuwa Kinshasa. Mulkin kama karya na Mobutu ya ci gaba har zuwa 1997 lokacin da ya tsere zuwa Moroko inda ya rasu.
Zakaran birnin Kinshasa
1974: shahararren dan damben Amirka Muhammad Ali a wata cibiyar samun horo da ke birnin Kinshasa. Ranar 30 ga watan Oktoba 1974 Muhammad Ali ya doke George Foreman a ajin masu nauyi a wani dambe mai muhimmanci. Kimanin mutane 60,000 suka shiga filin wasan da ke Kinshasa sannan wasu miliyoyi suka kalla ta akwatunan talabijin.
Muhammad Ali ya bar baya
Muhammad Ali tare da matasa. A cibiyar damben ta Muhammad Ali akwai yara maza da mata. Daya daga ciki ta shaida wa DW cewa "Ina gani kamar ni jikaryarsa ce na san abubuwa da dama game da shi". Ta ce wata rana ta so zama tamkar mutumin da ya zama mata madubi. Mai bayar da horo ya ce ana neman karin taimako daga ma'aikatar kula da wasanni.
Mutum mutumi na kula da zirga-zirgar motoci da samun hargitsi
Ba 'yan sanda ba, amma mutum mutumi ke kula da ababen hawa tun 2014 a yankin Asosa na tsakiyar birnin Kinshasa. Yana tura bayanai zuwa wata cibiyar da ake tantancewa. Akwai mutanen da suka samar da tsarin, wata kungiyar injiniyoyi ta Kwango da ke birnin Kinshasa.
Makon kayan kwalliya a Kinshasa
Bankwana da Paris, da New York da kuma Milan - Barka da safiya Kinshasa! Masu gwanayen kayan ado na zamani na Afirka sun gudanar da bikin mako a Kinshasa cikin watan Yulin shekara ta 2015. Marie-France Idikayi 'yar Kwango ta kaddamar da shirin ganin kayan Afirka sun yi tashe a duniya.
Karin shara na bukatar sabbin dabaru
Shara na zama wani bangare na birnin da ke dauke da mazauna kimanin milyan 10. Akwai yaran da suke neman kwalaben da za a iya sake sarrafawa. Suna kaiwa wajen da ake sabuntawa kamar wannan da wata kungiya mai zaman kanta ke tafiyarwa. Ga yaran haka ya zama hanyar samun 'yan kudaden shiga duk wata, sannan ga ma'aikata sun samu aikin yi.
Kinshasa 2016: Komai an yarda?
A karkashin gwamnatin Mobutu mai yiwuwa babu wanda zai yi tunanin haka: 'Yar wasa Julie Djikey, an yi tambaya ko mutum ya zama mota. 'Yar wasan ta kasa wa nononta bututu da mai a jikinta. Suna zanga-zangar nuna adawa da gurbata yanayi. Abin da suke yi suna zaburar da mata.
Kafin shekaru 50 Léopoldville ke zama sunan birnin Kinsahsa. Shi ne babban birnin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango wanda yake bin bayan biranen Lagos na Najeriya da Alkahira na Masar wajen yawan mutane a Afirka. Mazauna birnin suna karuwa. Birnin yana da cunkoson mutane akwai kuma masu zane-zane na zamani wadanda uske da karfin gwiwa. A wannan shekara ta 2016 Kinshasa ya cika shekaru 50 da samun suna.