1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 30 na mulkin Museveni a Yuganda

Umaru AliyuJanuary 26, 2016

Shugaba Yoweri Museveni na kasar Yuganda ya shiga jerin takwarorinsa biyar na nahiyar Afrika da suka shafe akalla shekaru 30 suna rike da mulki a kasashensu.

https://p.dw.com/p/1Hk34
Uganda Präsident Museveni
Hoto: AP

Mafi yawan al'ummar kasar Yuganda ba su san wani shugaban kasa ba a rayuwarsu, in banda Museveni, saboda daga cikin al'ummar Yuganda miliyan 35, kashi uku cikin hudu ba a ma haifesu ba lokacin da ya karbi mulki. Sakamakon mulkin nasa, abu ne da kowa ke iya gani a fili, da zarar an dubi halin da kasar da al'ummar ta suke ciki. Wannan dai shi ne ra'ayin Mareike Le Pelley, da ke shugabancin ofishin cibiyar Friedricht Ebert a Kampala babban birnin Uganda.

Ta ce "yan kasar yanzu sun yanke kaunar ko watan-watarana za su sami wani da zai maye gurbin Museveni da zai shugabancesu. Bayan mulkin shekaru 30, shugaba Museveni da jam'iyyarsa ta 'yan kishin kasa, ko kuma NRM a takaice, sun saje wuri guda sun zama daya yadda shike da wuya a iya gane banbanci tsakanin jam'iyya da ofishin shugaban kasa. Museveni ya nunar a fili cewar duk illahirin kudin Yuganda mallakarsa ne, kuma ba zai yarda a gudanar da wasu ayyuka na ci gaba a yankunan da ba su zabeshi ba".

Yoweri Museveni Vereidigung Präsident Uganda
Harkokin tsaro sun sa Museveni samun karbuwa a duniyaHoto: AP

Museveni ya kama mulki ne bayan da tun farko ya yi gwagwarmaya da shugabannin da ya ce ba sa son sauka su mika mulki ga wasu a kasashensu. Bayan yakin sari ka noke na shekaru masu yawa, Yoweri Museveni a shekara ta 1986 ya karbi shugabancin Yuganda bayan juyin mulki, abin da da farko ya kawo karshen rashin kwanciyar hankalin siyasa da yakin basasa da aka zub da jini mai yawa a lokacinsa. Da farko an sami zaman lafiya a kasar ta Yuganda, kuma tattalin arzikin kasar ya farfado. Sai dai shugaban bai yarda an gudanar da zabe ba sai bayan shekaru 10 a shekara ta 1996.

Museveni ya shimfida sabon kundin tsarin mulki, abin da ya maida Yuganda mai bin tsarin mulkin jam'iyyar siyasa daya. Ko da shi ke bayan shekaru 10, an sake yi wa kundin tsarin mulkin gyara, inda aka kyale ayyukan jam'iyyu masu yawa, amma an dage bangaren da ya baiwa shugaban kasa damar wa'adi biyu ne kawai kan mulki.

Museveni yace "tun shekara ta 1971 na ke cikin hali na gwagwarmaya. Shin kamata yayi in janye tun ayyukan da na fara ban karesu ba tukuna"?

Kalubalen tsaro da Moseveni ya fuskanta

Mulkin Museveni ya fuskanci barazana a shekaru na 1980, lokacin da mayakan kungiyar Lord Resistance Army, ko kuma LRA suka mamaye lardunan Arewacin Yuganda da yankuna na kasashen makwabta. Sa'annan daga baya ya shiga fama da mayakan kungiyar Al Shabaab, indahar yanzu sojojin kasar ta Yuganda suke a rundunar kasa da kasa tared a hadin gwiwar sojojin Kenya da Burundi domin kawar da mayakan na Al Shabaab.

Tun bayan harin cibiyar kasuwanci ta duniya a New York, shugaba Museveni ya kara wa kansa farin jini, lokacin da ya maida hankali ga abin da ya kira yaki da ayyukan tarzoma a yankin kahon Afirka. A shekarun baya-bayan nan ya kuma zauna kan teburin shawarwari a matsayin mai neman sulhunta rikice-rikice a kasashen Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango da Burundi. Hakan ya sanya Museveni ya dauke hankalin duniya kan dimbin matsalolin da ake fama da su a kasarsa, inji Mareike Le Pelley ta cibiyar Friedrich Ebert a Kampala.

Uganda Medienfreiheit Proteste 20.05.2013
'yan Yuganda ba su da cikakken 'yancin fadan albarkacin bakiHoto: Reuters

"Yan Yuganda da dama ba sa iya tuna shekaru na 1970 da na 1980, lokacin da Yuganda ta yi fama da yaki, saboda mafi yawansu sai bayan yakin ne aka haifesu. To sai dai ga 'yan Yugandan, rashin wuraren aiki shi ne babbar matsala. Idan kuwa har Museveni bai yi gyara a kan wannan ba, rashin gamsuwar matasan zai karu, matsaloli za su karu masa".

Le Pelley ta ce a game da 'yancin siyasa da walwalar jama'a kuwa, yanzu dai babu wani abin da ya rage a Yuganda bayan shekaru 30 na mulkin Yoweri Museveni.