1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 30 bayan kisan kare dangi mafi muni a Ruwanda

Binta Aliyu Zurmi
April 7, 2024

Akalla mutane dubu 800 ne suka hallaka a rikicin na kabilanci na Tutsi da Hutu a Ruwanda, wanda har yanzu ana gano manyan kaburbura makare da gawawakin mutane.

https://p.dw.com/p/4eVo0
Rwanda France Genocide Suspect Convicted
Hoto: Sayyid Abdul Azim/AP/picture alliance

Al'umma a kasar Ruwanda na jimamin ta'asar da ta faru a kasar ta tsakiyar Afirka shekaru 30 da suka gabata.

Mutane kusan dubu 800 ne yawancinsu yan kabilar Tutsi marasa rinjaye aka hallaka. 'Yan kabilar Hutu wadanda su ne mafiya rinjaye a kasar suka aikata ta'asar kisan gillar cikin kwanaki 100. Lamarin ya fara ne a ranar 7 ga watan Afrilun 1994.

Rikicin na ranar 7 ga watan Afirilu na zama mafi muni a tarihin fadan kabilanci, wanda har ya zuwa yanzu ana ci gaba da gano manyan kaburbura makare da gawawakin 'yan kabilar ta Tutsi.

Karin Bayani: Kagame ya shekara 20 a mulkin Ruwanda

Majalisar Dinkin Duniya na zama na musamman domin karrama mutanen da suka tsira daga wannan ta'asa.

A cewar sakatare janar na Majalisar Antonio Guterres ba za a taba mantawa da wannan bala'i na kisan kare dangi ba. 
Haka kuma ba za a manta da irin bajinta da juriyar da suka nuna ba.