Shekaru 200 na keke: Afirka na amfana!
A shekarar 1817 wani dan Karlsruher Karl Freiherr von Drais ya bayyana samfur farko na keke.Tun daga wannan lokaci ne keke ya fara samun karbuwa a sassa-sassa daban daban na duniya. Afirka ma ba a barta a baya ba.
Mozambik: Acaba don rage zaman banza
Fiye da mutane 2.000 na gudanar da sana'ar acaba a Quelimane, wani gari da ke arewacin Mozambik. Bisa dalilai na rashin aikin yi, dumbim matasa na zama 'yan kabu-kabu a wannan gari da ya kunshi mutane 200.000. Saboda haka farashin zirga-zirga ya yi kasa - sannan direbobi suka samu karancin kudin shiga.
Mozambik: Keken da ake sarrafawa
Yara a Maputo babban birnin kasar Mozambik na amfani da wannan salon keken-tsere da ake yin shi da waya. A gidan adana kayayyakin tarihi na "Global Players" a birnin Nuremberg , shi ne daya daga cikin manyan abubuwan da ke jan hankali. "Keke ya kasance wata alamar ci gaba ko ga matasa kuma su ma suna kerasu" a cewar masana.
DR Kwango: Karamci ga "Tshukudu"
A shatalai-talai da ke tsakiyar brinin Goma, an gina wani babban mutum-mutumi na katako da ake kira “Tshukudu” wato mai girma. Wannan alama ce ta wannan birni da yaki ya daidata. Direbobin keke “Tshukudu”1700 ne suka yi rejista a Goma, yayin da 3000 suke bayan garin na gabashin Kwango. “Tshukudu” na da matukar muhimmanci a titunan Goma.
Ghana: Keken da ya fito daga daji
A Accra babban birnin kasar Ghana, ana kera kashi 99 cikin 100 na kekuna ne da gwangala. Su na da kwari kamar karfe. Sannan suna sanya zukatan ma’abota hawa keke na duniya jin dadi. A daya daga cikin yarukan kasar a kan kirasu "Bambooseros". Wisdom Toxla da ke kera kekuna ya taba balaguro da irin wannan keke daga Accra a Kudanci zuwa Tamale a arewacin Ghana
Burundi: Jigilar da bata gurbata muhalli
Ko da a cikin biranen Afirka dako na bunkasa cikin hanzari. Amma kuma kai haja cikin sauri kuma a farashi mai rahusa ya kasance wani kalubale. A Cibitoke, wata unguwar da ke wajen birnin Bujumbura, ana amfani da kekuna ne wajen loda kayayyakin kamar katifu, domin tabbatar da an yi jigilar cikin tsari – kuma ba tare da gurbata muhalli ba..
Kamaru: zirga-zirga da keke cikin sauki
Wuraren da ake zirga-zirga da keke ba su da yawa a kamaru. Amma a Douala- cibiyar kasuwanci da ya kunshi mutane miliyan 2,4 an dade da fara amfani da keke. Sannan yana daga cikin biranen da aka fi amfani da keke a Afirka. Birnin ya kasance ginshiki a fannin sufuri a yankin Tsakiyar Afirka. Shugabannin wannan gari sun dade suna yi wa matuka keke alkawari ba tare da cikawa ba.
Malawi: Keke a matsayin "motar iyali".
A kewayen Muzuzu da ke zama birni na uku mafi girma a Malawi, akasarin iyalai na tafiye-tafiye ne kan keke. Wai ba sa cin karo da matsala? Garin na mike lambau, sannan gandun dajin yankin na da ban sha'awa. Gwamnatin Malawi na da niyyar alkinta garin domin jawo 'yan yawon bude ido. Za ta dogara kan ma'abota hawa keke na kasashen waje, wajen karfafa wannan tsari.
Tanzaniya: Keke ya kawo ci gaba!
A arewacin Tanzaniya, kusa da tafkin Victoria, jami'an wani karamin gurin kwana na amfani da kekuna wajen jigilar lemon kwalba. A ko da yaushe suna samun ci gaba. Ana jera kwalaben tare da dauresu da igiyoyi. Ba a kayyade yawan kwalaben ko Crake da ake jerawa a cewar mutane. Amma ba a jera fiye da 10 a kan keke daya.
Malawi: Gawayi a kan keke
Har tsawon kilometa 100 ake jigilar gawayi daga karkara zuwa biranen kudancin Malawai. A mafi yawancin lokuta ba a samun fiye da jakankuna biyu a wuraren dora kaya na keken idan ba a son taya ta fashe. Amma shi wannan matukin jakankuna uku ya dora kan keke, saboda haka ne yake turawa. A yanzu nauyin ya kai kilogram 240.
Mozambik: Keke i zuwa keken guragu
Wata yarinya da mahaifinta mai nakasa na sayar da taba sigari a daya daga cikin manyan titunan "Avenida Guerre Popular" na cibiyar tarihin Maputo da aka fi sani da suna "Baixa". Mahaifin ta ya kera wani keke me kujerar nakasassun domin samun damar zirga-zirga ba tare da neman taimako ba.