1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Mohammed na Moroko ya cika shekaru 20 a karagar mulki

Abdullahi Tanko Bala
July 30, 2019

Sarki Mohammed na shida ya cika shekaru 20 kan karagar mulki, a zamaninsa ya bai wa kasar cikakken yanci ta fuskar siyasa baya ga aiwatar da sauye-sauye da suka dora Moroko kan tafarkin zamani bayan ya gaji mulki.

https://p.dw.com/p/3N09u
Marokko König Mohammed VI in Rabat
Sarkin Moroko Mohammed na shida yana tafiya yayin wani wani buki a Rabat 2016Hoto: Getty Images/C. Jackson

A lokacin da sarkin Moroko ya rasu, gidajen radiyo da talabijin sun katse shirye-shiryensu inda suka rika sanya karatun alkur'ani bayan da aka bada sanarwar rasuwar sarki Hassan na biyar a ranar 23 ga watan Yuli 1999. Dubban 'yan kasar Moroko sun yi layi akan tituna domin yin bankwana da sarkinsu yayin da aka dauko shi a cikin makara lullube da bakin kyale da aka rubuta ayoyin kur'ani da dinkin surfani.

Shugabannin kasashe da dama sun bi sahun jama'ar kasa wajen yin bankwana da sarki ciki har da tsohon shugaban Amirka Bill Clinton da Firaministan Israila na wancan lokaci Ehud Barak da kuma marigayi shugaban Falasdinawa Yasser Arafat.

Yan kwanaki bayan rasuwar sarkin a ranar 30 ga watan Yuli aka nada babban dansa Mohammed na shidda a gadon sarautar. A wannan rana matashin sarkin ya fara zuwa masallaci yayi sallar Juma'a. Daga nan kuma ya yi jawabinsa na farko ga al'umma inda ya nesanta kansa daga ginshikin siyasa na mahaifinsa.

Aiwatar da sauye-sauye ga tsarin sarauta.

König Mohammed von Marokko mit Kindern
Sarki Mohammed a tsakiya yarima Moulay Hassan a dama Moulay Rachid a hagunHoto: picture-alliance/dpa

Kwamitin tantance gaskiya da sarki Mohammed ya kafa a shekarar 2004 da nufin tantance keta haddin bil Adama da aka yi a zamanin mulkin mahaifinsa ya baiwa wasu da dama takaici.  Ko da yake an gano abubuwa da dama da aka aikata a wancan zamani amma ba a hukunta wadanda suka aikata din ba.

Hakan bai hana sarkin aiwatar da manufarsa ta zamanantar da kasarsa ba. Ya kaddamar da sabuwar dokar zamantakewar iyali wadda ya dabbaka tun shekarar 2004. Wannan ya karfafa wa mata, misali samar da daidaito tsakanin maza da mata inda a yanzu mace za ta ke da yancin saki wajen mutuwar aure wanda a da namiji ne kadai yake da wannan dama.Kuma maimakon maluman musulunci a yanzu alkalai ne suke shari'a kan rabuwar aure.

Ta hanyar sauye-sauye irin wannan, sarkin ya sami goyon bayan masu sassaucin ra'ayi abinda ke zama mai tasiri idan aka kwatanta da adawar da masu kaifin kishin Islama da kuma tasirin da suke da shi akan matasa wadanda suke jin cewa an mayar da su saniyar ware a cikin al'umma ta fuskar tattalin arziki da siyasa.