1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Ana tunawa da harin 11 ga watan Satumba

Salissou Boukari MNA
September 10, 2021

Shekaru 20 bayan harin ta'addanci da aka kai a kasar Amirka wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuwar jama’a da dama, sannu a hankali ta'adanci ya watsu a sassa dabam-dabam na duniya.

https://p.dw.com/p/40BBm
USA - 20. Jahrestag der Terroranschläge
Hoto: Alex Brandon/AP/picture alliance

Tun hare-haren ta'addancin da aka kai wa Amirka a ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, lokacin da ana kallon lamari a can wani yanki na duniya, sai sannu a hankali wannan matsala ta ta'addanci ta sauka a yankin Sahel somawa daga kasar Mali, inda shekaru 11 bayan harin na Amirka 'yan ta'adda suka mamaye kasar Mali tare da kai hare-hare. Sannu a hankali abin ya yi kamari a yankin na Sahel. To ko daga ina ta'addanci a yankin Sahel ya samu asali? Abas Abdoulmoumouni Masani kan harkokin ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel ya nuna cewa: "Rushe jam'iyyar FIS a Aljeriya ya sa ta koma kungiyar daukar makami ta GIA. Ita ce da ta yi karfi ta yadu cikin yankin Sahel, inda cibiyar ke a kasar Mali, suna kuma aikace-aikace a kasashen Burkina Faso da Nijar."

Karin Bayani: Waiwayen dangantakar Jamus da Afirka

Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Rikicin ta'addanci dai a yankin na Sahel za a iya cewa ya samu gindin zama bisa dalilai da dama, ganin cewa nan ne kuma aka samu wani kwararo da masu safarar miyagun kwayoyi da safarar mutane ke bi, sannan ga safarar makamai. Ba yau ne ake ruwa kasa na shanyewa ba, ba y u ne ake zaman nemo bakin zaren warware wannan matsala ta ta'addanci a yankin Sahel ba, ganin cewa har an kafa rundunoni da dama da za su yaki ta'addanci baya ma ga dakarun kasashen waje dubbai da suke yankin na Sahel a karkashin Majalisar Dinkin Duniya da Faransa.

Sai dai kuma a cewar Honorable Hama Assa, wanda a baya ya jagoranci kwamitin tsaro na majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar dole fa kasashe su tashi tsaye: "Ya kamata masu tallafa wa 'yan ta'adda a gane su su kuma daina. Zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasar tattalin arziki za su samu ne idan bindiga ba ta motsa ba. Da ma wannan yanki na Sahel yana fama da matsalar talauci. Dole a hada karfi da karfe tsakanin kasashen wannan yanki domin a gudu tare a tsira tare."

Karin Bayani: Za a janye Barkhane daga Sahel

Mali I Symbolbild I Lage in Diabaly
Hoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Yanzu haka dai za a iya cewa 'yan ta'adda sun fitar da sabon salo na kai hare-harensu ga fararan hula, a wani mataki na saka tsoro da rudani a tsakanin al'ummar karkara ta yadda a sassa dabam-dabam suka hana a yi noma a wannan lokaci na damina, lamarin da ke gaskata zaton da wasu masharhanta ke cewa yan ta'addan na son su samar da wani yanki nasu ne a tsakanin kasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali tare da samun hanyar da ba ta da wani cikas har ya zuwa kasashen Libiya da Aljeriya.