1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 100 da duniya ta san jarumi James Baldwin

Usman Shehu Usman M. Ahiwa
August 2, 2024

James Baldwin wani fitaccen marubuci ne Ba'Amurke mai asalin Afirka wanda a ranar biyu ga Augstan nan ya cika shekaru 100. Tarihi dai ba zai manta da jarumi Baldwin ba.

https://p.dw.com/p/4j3D2
Marigayin marubuci James Baldwin
Marigayin marubuci James BaldwinHoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com/Globe Photos

An haifi James Baldwin a unguwar matalauta da ake kira Harlem da ke gefen birnin New York. A lokacin ya tashi cikin unguwar matalauta wadanda ke tsakiyar fiskantat tsanainin wariyar jinsi. Bayaga talauci ahaka kuma tsiraru bakaken fata a lokacin suna dandana acabar yan sanda. René Aguigah Danjarida ne kuma Marubuci ne Wanda ya rubuta tarihin James Baldwin. Wanda yace dan fafitikar ya kasance wata fitallah ga Afirka.

James wanda ya taso a gidan da yake matsayin agola, wato a hannun Bappansa wanda ya auri mahaifiyarsa bayan rabuwar su da mahaifiyarsa, kuma ya tsinci labarin ukubar da mutanen gidansu suka sha a hannun fararen fata da ke kin jinin bakar fata a lokacin. Irin labaran da ya samu sun yi matukar jan hankalinsa, domin shi rukuni na biyu ne daga iyayensa na wadanda suka zo Amurka. Irin rawar da ya taka wajen jagorantar yaki da wariyar jinsi su ne suka sa marubuci René Aguigah ya ce shi ma dole ya ba da tasa gudumawa.

‘‘A gare ni, akwai wani dan abin mamaki na rashin bambance-bambance a cikin wannan batun na Afirka, lokaci zuwa lokaci abun na fado min; kuma wannan tabbas yana cikin abin da ke tattare da Baldwin, wato batun Afirka shi ne farko.

Ayyukan Baldwin sun yi matukar karbuwa a hannun marubuta inda rubuce-rubuce irin nasa, suka yi matukar jawo hankalin duniya kan tasirin Afirka.

Afirka ta kara zama abar sha’awa ga marubuta musamman a cikin littatafai na farkon shekarun 1950 da kuma a cikin litattafai na karshen shekarun 1970. Haka ma abubuwa da dama sun faru a tsakanin wadannan shekaru, kuma an samu gagarumin sauyin daga cikakkiyar siffar Afirka da a baya ake daukanta tabbas an samu sauyi. Misali lokacin za a ce kasashen Senegal da Ghana da dai sauransu."

 James Baldwin tare da Mr. Brando
Hoto: Rowland Scherman/Imago Images

Shi dai James Baldwin gwagwarmayarsa ce ta jawo hankalin Amurkawa bakar fata, inda bisa yadda ya ga rayuwa anguwarsu, sai ya nuna cewa shi kam yana da damar kawo sauyi, inda ya dukufa wajen tsara rubuce-rubucen cewa bai amince da wariyar da ake nuna wa babaken fata ba, abin da sannu a hankali ya watsu daga birnin New York i zuwa wasu sassan kasar ta Amurka.

Kuma ya yi matukar fice a Amurka da Turai da Afirka, don haka duk lokacin da aka tabo yaki da wariyar jinsi, to kusan dole ne a ambaci fafutikar da ya yi.