Shekaru 10 da jibge shara mai guba a Abidjan | Zamantakewa | DW | 17.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shekaru 10 da jibge shara mai guba a Abidjan

Har yanzu kamfanin kasar Panama da ya zubar da wannan guba bai kai ga cika alkawarin biyan diyya ga mutane da lamarin ya shafa ba.

A kasar Cote d'Ivoire shekaru goma bayan afkuwar badakalar zubar da dagwalan masana'antu mai guba da wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Panama mai suna Probo Koala ya yi a wasu unguwannin kewayen birnin Abidjan, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a yayin da wasu suka samu nakasa, har yanzu kamfanin da ya zubar da wannan shara mai guba bai kai ga cika alkawarin da ya yi na biyan kudaden diyya ga mutane da lamarin ya shafa ba.

A daran 18 ga watan Agustan shekara ta 2006 ne dai jirgin dakwan man fetur din mai suna Probo Koala na kasar ta Panama wanda wani kamfani na hadin gwiwar kasar Holland da kuma Switzerland mai suna Trafigura ya doro wa hajar dagwalan masana'antun mai guba ya zubar da haramtacciyar hajar tasa a wasu unguwannin kewayen birnin Abidjan babban birnin kasar ta Cote D'Ivoire.

Ha'inci wajen aikin kwashe dagwalan

Giftmüll Probo Koala

Kwamishinan muhalli na EU Stavros Dimas (tsakiya) na magana da manema labarai

Bincike ya gano cewa ton dubu 581 na dagwalan masana'antun jirgin ruwan ya zubar a wurare 17 na birnin Abidjan da kuma musamman a wurin tattara shara na unguwar Akouedo. Abin kuma da ya yi sanadiyyar mutuwar a hakumance mutane 17 a yayin da warin gubar ya haddasa cututtuka ga dubunnan mazauna birnin. Shekaru 10 bayan afkuwar wannan lamari mazauna unguwar Akouedo sun ce har yanzu warin gubar na ci gaba da addabarsu domin kuwa aikin kwashe dagwalan da aka yi an yi ha'inci wajen yinsa. Wani mazaunin unguwar cewa ya yi.

Ya ce: "Yanzu haka da an yi ruwan sama sai wari ya turnuke kauyen namu na Akouedo. Abin da ya sanya lokaci zuwa lokaci muke fama da rashin lafiya. Wasu daga cikin mata masu juna biyu da suka shaki iskar gubar sun yi raggon kaya wasunsu kuma cikkunan nasu sun zube, a yayin da wasu suka haifi 'ya'ya da nakasa wacce suke dauke da ita har yanzu. Abin na yi mana illa sosai."

Hanyoyin lumana don samun mafita

Containerschiff Probo Koala

Jirgin ruwa Probo Koala da ya jibge dagwalan masana'antu a kusa da Abidjan a watan Agustan 2006

Domin warware wannan matsala ta hanyar lumana da kuma kaucewa kalubalen shari'a kamfanin Trafigura ya dauki alkawura dabam-dabam da suka hada da gina gidan asibiti na musamman domin kula da lafiyar mutanen da suka shaki gubar. Kuma a wancan lokaci gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta karbi kudi tsaba miliyan dubu dari daga hannun kamfanin da sunan biyan diyya ga mutanen da lamarin ya shafa. Sai dai shekaru 10 sun shude ba tare da samun ko da dala ba. Kuma Abel Djeket shugaban matasan kauye na Akouedo wanda ke fama da matsaloli na sheda da kuma cutar kyansar fata sanadiyyar shakar gubar ya nuna damuwarsa yana mai cewa:

Ya ce: "Mun gaji da halin da muke ciki amma domin ba mu da 'yanci, mun rasa tudun da za mu dafa don haka mun hakura muna kallon gwamnati kawai, a yayin da a share daya mutanenmu na ta mutu a kowace rana ta Allah. Abin takaici ne."

Yanzu dai mutanen da wannan matsala ta shafa na fatan ganin albarkacin ranar zagayowar cikon shekaru 10, gwamnati za ta dube su da idon rahama domin basu wani abu daga cikin hakkokinsu da ke a wurinta.