1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 10 bayan durkushewar Lehman Brothers

Abdullahi Tanko Bala
September 15, 2018

Shekaru goma kenan cif da Bankin Lehman Brothers shahararren bankin zuba jari mafi girma a duniya ya sami karayar arziki da ya kai ga durkushewarsa baki daya.

https://p.dw.com/p/34vWr
New York City Lehman Brothers Zentrale
Hoto: Getty Images/M. Tama

Shekaru goma kenan cif da Bankin Lehman Brothers shahararren bankin zuba jari mafi girma a duniya ya sami karayar arziki da ya kai ga durkushewarsa baki daya, lamarin da ya kasance farkon matsalar tattalin arziki mafi muni da duniya ta fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu

Tattalin arzikin Amirka ya shiga tangal tangal yana kuma bukatar ceto. Wannan shine bayanin da sakataren baitulmalin Amirka Ben Bernanke ya yiwa majalisar dokoki a wancan lokaci. To amma yadda za a shawo kan matsalar shine jidali, saboda matsaloli ne da yawa suka taso a lokaci guda musamman karyewar kasuwar gidaje.

New York City Lehman Brothers Zentrale
Hoto: picture-alliance/AP Photo/L. Lanzano

Tattalin arzikin Amirkar ya shiga halin tsaka mai wuya inda hannayen jari suka karye, aka kuma yi hasarar dukiya da ta kai kusan Dala trillion bakwai sannan cikin shekaru biyu Amirkawa kusan miliyan tara suka rasa ayyukansu.

Shawarar Bernanke ita ce a yi sassauci a manufofin kudade. Manyan Bankunan kasashe a fadin duniya sun rage kudin ruwa sannan suka kara yawan kudi a kasuwa da fatan cewa bankuna za su bada bashi da saukin ruwa domin farfado da tattalin arziki. Shawarar ta yi domin tattalin arzikin ya farfado.

Kamfanonin Amirka sun bada labarin samun riba mai gwabi. A yan makonnin da suka gabata wasu kamfanoni biyu na Amirka Apple da Amazon sun sanar da samun gagarumar riba. Shugaban Amirka Donald Trump ya ce suna fatan samun gagarumin sakamako na farfadowar tattalin arziki

'Yan lokuta da suka wuce alkaluman cigaban tattalin arzikin Amirka da aka fitar na abin da take samu a shekara sun karu kuma ina farin cikin sanar da cewa a kashi na biyu na sulusin wannan shekarar tattalin arzikin Amirka ya bunkasa da adadi mai armashi na kashi hudu da digo daya cikin dari. Muna kan hanyar samun bunkasa mafi girma a shekara wanda ba a sami irinsa ba cikin shekaru goma sha uku da suka wuce, muna kuma fatan samun cigaba fiye da wadannan alkaluma

Wall Street Zinserhöhung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Drew

Ita kanta ma'aikatar kudi ta Amirka ta sha baiyana kwarin cewa tattalin arzikin zai farfado sai dai bayan kawo karshen matsalar koma bayan tattalin arzikin al'amura basu koma daidai ba, domin kuwa matsalar ta kau amma ta bar dumbin bashi.

Bashin da ke kan kasashe a duniya baki daya ya karu zuwa kashi 74 cikin dari a karshen shekarar 2017 kwatankwacin dala trillion 247.

Itay Goldstein masanin tattalin ariki ne kuma malamai a jami'ar Pennslyvania. Ya yi tsokaci yana mai cewa:

Kasuwar hada hada da basuka sun hadu sun gauraye da matsalolin tattalin arziki baki daya. Mun ga irin yadda aka sami karuwar cin bashi sakamakon koma bayan tattalin arziki.

A hannu guda dai manufar soke kudin ruwa na da nasa matsalar, yayin da ake samun karuwar riba a waje daya kuma akwai hadarin yiwuwar karya alkawarin bashin sakamakon matsalar da aka shiga.