Shekarar 2014 ta kasance mafi zafi a duniya | Labarai | DW | 02.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekarar 2014 ta kasance mafi zafi a duniya

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da yanayi da kuma binciken sararrin samaniya OMM,ta sanar da cewar shekarar ta kasance mafi gumi.

A cikin rahotonta na shekara da ta bayyana hukumar ta ce kusan kishi 93 cikin ɗari na tsananin zafin da aka yi a shekarar da ta wucce. Ɗan Adam shi ne sanadinsa saboda ɗumamar yanayi da yake janyowa ta hanyar sare dazuzzuka da kuma yawan hayaƙi na iskan gas da kamfanoni ke fitarwa.

Shugaban hukumar mista Michel Jarraud ya ce lamarin na tsananin zafin shi ne ke janyo mummunar ambaliyar ruwan sama da kuma wasu sauran bala'oiin da ke da nasaba da yanayin. Hukumar ta OMM ta bayyana wannan rahoto ne a jajibirin babban taron da za a gudanar a makon gobe a kan canjin yanayi domin samun sulhu tsakanin ƙasashen duniya.