Shekara guda da tsare Moussa Tchangari a Nijar
December 3, 2025
Kungiyar ta Alternative ce dai da sauran abokan arziki da sauran abokan kokawa na kungiyoyin fararan hula suka hallara domin tunawa da dan gwagwarmayar Moussa Tchangari da a wannan Laraba ya cika shekara guda cif da kamun da aka yi masa, inda bayan shafe kimanin wata daya a ofishin jami'an tsaro masu yaki da ayyukan ta'addanci aka kuma fice da shi ya zuwa gidan kaso na garin Filingue da ke da nisan kimanin kilomita 180 da birnin Yamai.
'Ya'yan Moussa Tchangari Falmata da Ya Kaka Mariama, su ne suka soma da ba da bayani kan tarihin mahaifinsu wanda ya shafe dukkannin lokacinsa a kokawar kare hakkin masu karamin karfi ko tsiraru, wanda ta dalilin haka ya sha fuskantar kamu da gurfana a gidan kaso daban-daban na kasar Nijar. Falmata moussa Tchangari ta ce suna cike da kwarin gwiwa, kaman mahaifinsu.
An samu halartar wakillan wasu kungiyoyin fararan hula da suka zo domin tunawa da nuna alhinin kan ci gaba bda tsare dan gwargwarmaya Moussa Tchangari wanda yau shekara guda a daure gidan yari.
An dai yi gangamin ne a gaban dukkannin iyalan Moussa Tchangari musamman mai dakinsa Fati da kalaman da ake furtawa na tunawa da mijinta duk da ba mutuwa ce ya yi ba, suka sanya ta tare da mutane da dama zubar da hawaye tare da yin addu'o'i na ganin an sallamo Moussa Tchangari ya dawo cikin iyallansa.