Shekara guda da fara rikicin Tigray
Har yanzu ba alamun kawo karshen rikicin Habasha da aka fara shekara guda da ta gabata, inda duk bangaorin ke zargin juna da irin kalubalen da jama'a ke fuskanta.
Birni cikin rudani
Mazauna Mekele babban birnin na binciken kayansu cikin baraguzan gine-gine bayan da dakarun gwamnati suka kai hari ta sama kan gidajensu a ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata. Sojojin kasar sun ce sun kai harin ne don afkawa wata masana'anta da ake yin makamai wadda suka ce mallakin TPLF abin da suka musanta.
Hayaki sanadiyar tashin bam
Wannan hayaki ne a kan titin Mekele bayan wani hari da sojoji suka kai. Mayakan Tigray sun zargi dakarun gwamnati da kisan fararen hula yayin da gwamnatin tarayya ke cewa tana kai hare-hare kan rumbunan adana makamai na 'yan tawaye. Mazauna yankin sun ce an lalata wata masana'anta guda a Makele din.
Dakarun da aka kame
Nan sojojin Tigray ne a zaune bayan da dakarun gwamnati suka kamesu, inda suke jiran a kai su wurin da za a tsaresu a cikin watan Oktoban da ya kamata. Gabannin tafiya ta da su wajen da za a tsaresu, sojoji sun yi ta kewaya da su cikin Mekele a wani yanayi na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.
Taimako na tafe
Motar kungiyar bada agaji ta Red Cross ta shiga Mekele don bada agaji bayan wani hari da aka kai da jiragen yaki na soji. 'Yan Red Cross din na aiki ne don agazawa al'umma tare da nema musu matsugunai a yankin Tigray. Har wa yau 'yan kungiyar na taimakawa wajen bawa jama'a dama ta yin magana da 'yan uwansu ta waya bayan da hukumomi suka katse kafofi na sadarwa.
Samar da kayan agaji
Nan jigin daukar kaya na kungiyar agaji ta Samaritan's Purse na sauke kayan agaji a filin jirgin saman Mekele a watan Maris din da ya gabata. Harkar shigar da kayan agaji Tigray ta fusknaci tsaiko sosai bayan da aka sanya shigaye na binciken ababan hawa, inda ake dakatar da motocin da ke dauke da kayan agaji yayin da hare-hare ta sama ke dakatar da wasusu daga shiga yankin.
Bukatar neman agaji
Ma'aikatan lafiya sun yi zanga-zangar lumana a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Mekele, inda suka yi tir da abin da ya sa aka samu karancin magani da abinci da ya haifar da rasuwar marasa lafiya. Rahotanni sun ce kayan abinci na jibge a babban birnin kasar daidai lokacin da yara masu yawa ke fama da tamowa. A baya-bayan nan MDD ta ce za ta janye rabin ma'aikatanta daga Habasha.
Wadanda yaki ya shafa
Nan wata ce da harin da aka kai Togoga ke karbar magani a asibiti. A ranar 22 gawatan Yunin da ya gabata ne mayakan Habasha suka kai hari ta sama a garn na Togoga a ranar kasuwa. Harin ya yi sanadin rasuwar mutane 64 tare da jikkatar wasu 184. Da fari an dakatar da shigar motocin daukar marasa lafiya da suka yi yunkurin shiga yankin amma daga baya wasu sun samu shiga.
Zanga-zanga a kasashen duniya
Mutane a kasashen duniya sun gudanar da zanga-zanga ta nuna goyon baya ga 'yan Tigray cki kuwa har da wadda aka yi Whitehall da ke Landan a ranar 19 ga watan Oktoban da ya gabata. Mutanen sun yi ta daga tutoci da rera take na kin jinin abin da ke faruwa kana sun yi kira da a daina rikicin da kuma killace yankin da aka yi. Galibin masu zanga-zangar 'yan Habasha ne.
Fushi daga kowane bangare
Masu zanga-zanga a Addis Ababa babban birnin Habasha sun hadu a wajen ofishin Shirin Samar da Abinci na MDD a watan Satumba da ya gabata don nuna rashin jin dadinsu da tura kayan agaji yankin Tigray. Gwamnatin Habasha dai ta ayyana TPLF a matsayin kungiyar 'yan ta'adda yayin dajami'an gwamnati da 'yan fafutuka a nasu bangaren suka ce TPLF din na aikata laifuka manya ciki har da sa yara aikin soji