Shekara guda bayan zaɓe a Tunisiya | Siyasa | DW | 31.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda bayan zaɓe a Tunisiya

Zaɓen dai ya kasance wata dama ce ga al'ummar ƙasar na fitowa domin gudanar da 'yancinsu na 'yan ƙasa wajen zaɓar waɗanda suka cancanci wakiltar su.

Duk da cewar an samu nasarar gudanar da zaɓe a karon farko a tarihin Tunisiya dai har yanzu da sauran rina a kaba. Domin a kusan a kowace rana dubban ɗaruruwan mutane na gudanar da gangami a fƙasar ta Tunisiya dake da yawan al'umma miliyan 10. Kazalika ana ci gaba da gudanar zaman dirshan da zanga-zanga. Tattalin arzikin ƙasar dai na ci gaba da durkushewa, yayainda kawao yanzu ba'a kammala rubuta kundun tsarin mulkinta ba. Masu mulkin ƙasar na cigaba da zama cikin fargaba na masu tsananin kishin addinin Islama da kuma yiwuwar gurguncewar madafan iko da suke da ita. Musamman ayayin da magoya ɓangarorin biyu ke ci gaba da bazama tituna suna ƙarfafa goyon bayansu.

Dubban mutanen dake zanga zanga kenan a dandalin taro na Bourguiba dake birnin Tunis, suna cewar Allah wadan sojoji. Ko a makon daya gabata sai da aka gudanar da irin wammam gangamin adawa a kofar ma'aikatar harkokin cikin gida na tunisiya. Ga dai a bunda masu zanga-zangar ke cewa.

"A karon farko a bara na kaɗa ƙuri'a ta, kuma cikin alfahari. Duk wani tsoro ya kau daga zuciyata".

" Idan har muka cimma nasarar wannan zaɓe, tare da tsare ƙuri'unmu, zan iya cewar mun cimma nasara shiga tafarkin Demokradiyya, kuma a zaɓe na gaba al'ummar Tunisiya zasu juyawa masu ra'ayin addinin islama baya".

Tuni dai magabatan ƙasar ta Tunisiya suka yi kira da kawo ƙarshen wannan zanga zanga, da a cewarsu ba zai kai ƙasar ko'ina ba. Priminista Hamadi Jebali ya bukaci ɓangarorin biyu da su maida zuciya nesa, domin ƙauracewa sake jefa ƙasar cikin tarzoma.

Bukin cika shekara guda da nasarar gudanar da zaɓe a Tunisiya dai Ya zo ne a daidai lokacin ake ci gaba da tayar da jijiyar wuya tsakanin gwamnatin haɗaka dake ƙarkashin jagorancin jam'iyyar su Jabali masu ra'ayin kishin addini ta Ennahda da 'yan adawa.

Manazarta dai sun sha sukar lamirin gwamnatin mai ra'ayin addinin musuluncin da rashin inganta rayuwar al'ummar ƙasar tun bayan juyin juya halin daya kawar da gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali a watan Janairun 2011.

Masu goyon baya da adawa da gwamnatin Tunisiyan dai suka yi gangami a majalisar kasar, inda masu adawar ke kira ga sabon juyin juya hali, su kuwa magoya bayan Ennahda suna Allah wadan shugaban adawa Beji Caid Essebsi, wanda suke wa kallon ɓurɓushin tsohuwar gwamnatin da aka hamɓace. Ga dai abunda Shugaban adawa Essebsi yake cewa.

"A yau muna ɗanɗana kunaɗarmu sakamakonm wahalhalun da mukayi na juyin juyin , muna biyan muradin mu na komawa tafarkin demokraɗiyya da jininmu. Mutuwar ɗan uwanmu, shine kisan gilla na siyasa na farko da aka yi a Tunisiya bayan juyin juya hali".

Mutuwar ɗan adawar dai ya haifar da sabon saɓani tsakanin gwamnatin haɗakar Tunisiyar dake da rinjayen jam'iyyar masu sassaucin ra'ayin addinin musulunci na Ennahda da ɓangaren 'yan adawa.

Babbar matsalar al'ummar Tunisiyan dai itace durkushewar tattalin arziki, daura da matsalar rashin aikin yi da kai a kalla kashi 50 cikin 100. Gashi har yanzu Tunisiya bata da kundin tsarin mulki.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal