1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda bayan Tsunami

Hauwa Abubakar AjejeDecember 26, 2005

Kasashen duniya na gudanar da adduoin zagayowar shekara guda da abkuwar balain Tsunami

https://p.dw.com/p/Bu34
Hoto: AP

Shekara guda guda da abkuwar wannan balain ambaliyar tsunami,har yanzu dubban wadanda suka tsira daga balain suna cikin bakin ciki da tsoron sake abkuwar wannan musiba,duk kuwa da taimako da suke samu daga masu bada gudumowa.

Girgizar kasa na karkashin ruwa da karfinsa ya kai 9.15 a maunin richter a tsibirin Sumatra,mafi karfi cikin shekaru 40,ya haddasa wannan ambaliyar a kasashen dake bakin iyaka tekun Indiya daga kudancin Asiya zuwa gabashin Afrika.

Igiyoyin ruwa da tsawonsu ya kai taku 33 da suka biyo baya,sun kwashe daruruwan mutane dake shakatawa a bakin kogunan yankin,sun lalata gidaje tare da share kauyuka da tsibirai dake kan hanyarsu a Aceh,Sri lanka,India da kudancin Thailand.

Wani saurayi dan shekaru 19 mai suna Janenthra a Sri lanka,yace,shekara guda har yanzu muna tuna wadanda suka mutu,da dukiyoyi da suka salwanta,da rashin aikin yi a yanzu,yace har yanzu muna cike da tsoron sake abkuwar ambaliyar tunda yanayin daminar bana dai dai yake da bara.

Akalla mutane fiye da dubu 230 ne suka halaka cikin ambaliyar data gudana a kasashe 13 dake kusa da tekun Indiya,kusan kashi 3 bisa hudu kuwa a Aceh ne,kusa da tsibirin Sumatra.

Hakazalika mutane kusan miliyan daya da dubu dari takwas sun rasa matsugunansu.

Wajen adduoin tunawa da wadanda suka halaka,shugaban kasar Indonesia Bambang Susilo,yace,yayinda ake tunawa da wadanda suka rasu,yanzu lokaci yayi da sauran jamaa zasu ci gaba da rayuwarsu,yace lokacin ne daya kamata a taimakawa wadanda suka tsira sake farfado da yankunansu da kuma aiyukansu.

Shugaban kasar, mafi yawan jamaa na uku a duniya ya kuma godewa kasashen duniya da kungiyoyi da suka taimaka,amma yace har yanzu akwai sauran aiki.

Majalisar Dinkin Duniya tace kasashe da kungiyoyi sunyi alkawuran bayarda taimako da kudinsa ya kai dala biliyan 13 da miliyan dubu 6,taimako mafi girma da aka taba yi a tarihi.

A yau din nan a garin Peraliya dake kudancin sri lanka,mabiya addinin Hindu,Kirista Buddha da Musulmi sun gudanar da aduoii a yankin da mutane 1000 suka halaka lokacinda ambaliyar ta tuntsurar da jirgin kasan da suke ciki.

A kudancin Thailand kuma,jamaa da dama daga bangarori dabam dabam na duniya,sun hallara wajen tunawa da kusan mutane 5,395 da aka tabbatar sun halaka da wasu 3000 da suka bace a Thailand.

Wata mata yar kasar Australia mai suna Joy Vogel,wadda ‘yarta mai cikin wata 3 ta halaka tare da wasu yan kasar waje su kusan 2000 cikin ambaliyar tace,har yanzu,tana ganin kamar mafarki ne wannan ambaliyar,amma tace tana ganin har yanzu suna tare da wadanda suka halakan.

Kamar sauran yan uwan wadanda suka halaka a tsunami,Vogel, ta shiga gadan gadan cikin shirinn taimakon wadanda suka tsira daga balain ambaliyar ruwa ta tsunami.