1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara 50 da kisan Martin Luther King Jr

Mohammad Nasiru Awal RGB
April 3, 2018

A ranar 4 ga watan Afrilun shekarar 1968 shekaru 50 ke nan da wani dan wariyar launin fata a Amirka, James Earl Ray ya harbe dan rajin kare hakkin jama'a kuma bakar fatar Amirka, Martin Luther King Junior, har lahira.

https://p.dw.com/p/2vQeJ
USA Martin Luther King Jr. - Rede "I have a dream", 1963
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Har yanzu shekaru 50 bayan aukuwar wannan lamari, kalaman Martin Luther King Junior na zama abin da ke burge mutane da yawan gaske, musanman jawabinsa kan karfafa 'yanci bakar fata da ya sa ya shiga kundin tarihi. A jawabinsa na "I have a dream" da ya ke cewa, "Ina fata 'ya'yana hudu za su girma a wata kasa da za a dubi halinsu a yanke hukunci amma ba launin fatar jikinsu ba."

Da wadannan kalaman da Martin Luther King Jr. ya yi a gaban wani gangami na fiye da mutum dubu 250 ciki har da fararen fata a birnin Washington a ranar 23 ga watan Agustan 1963, ya shiga kundin tarihi. Burinsa shi ne karfafa 'yancin bakar fata dangane da matsalolinsu na yau da kullum da ma yadda suke fuskantar matsala wajen neman aikin yi.

An haife shi a ranar 15 ga watan Janerun 1929 a birnin Atlanta na jihar Georgia, da sunan Michael King Jr. Mahaifinsa fasto ne mahaifiyarsa kuma malamar makaranta. Tun yana karami ya fuskanci wariyar launin fata, amma duk da haka bai karaya ba, ya yi karatu har ya kammala jami'a a fannin ilimin halayyar zaman jama'a da na addinin Kirista. Sai dai mahaifinsa ya canja masa suna bayan ziyarar da ya kai birnin Berlin a 1934 lokacin da ya sadu da dan rajin sauyin addinin Kiristan nan Martin Luther.

Martin Luther King Jr. ba addini kadai yake sha'awa ba, ya kuma yi koyi da wasu fitattun mutane kamar Aristoteles, Plato da Marx da kuma Mahatma Ghandi musamman dangane da gwagwarmaya cikin lumana. A 1953 ya auri Coretta Scott Williams da suka samu 'ya'ya hudu da ita. Dan kwatar 'yancin ya yi bakin jini ba kawai a wajen wasu daga cikin fararen fatar Amirka masu akidar wariya ba, sun sha sa kafar wando guda da hukumar binciken manyan laifuka ta tarayya wato FBI wadda ta zarge shi da yada ra'ayin kwaminisanci.  A ranar 4 ga watan Afrilun1968 wani mai aikata laifi farar fata dan wariyar launin fata wato James Earl Ray ya harbe Martin Luther King Jr. har lahira a gaban wani otel da ke birnin Memphis na jihar Tennessee. Ya mutu yana da shekara 39 a duniya.