Shawarar kwamitin sulhun MDD ga Masar | Labarai | DW | 16.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shawarar kwamitin sulhun MDD ga Masar

Manbobin 15 na Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suka y zama na musamman sun yi kira ga bangaraorin Masar da ke gaba da juna da su kai hankali nesa.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa a birnin New-York domin yin nazarin rikicin siyasa da kuma mummunan tashin hankali da kasar Masar ta tsinci kanta a ciki. Kasashen Austreliya da Faransa da kuma Birtaniya ne suka bukaci a shirya wannan taron da ya gudana a cikin siiri. Sama da mutane 600 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu a ranar labara da ta gabata bayan da sojoji suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa magoya bayan hambararen shugaba Mohammed Morsi daga wuraren da suke gudanar da gangami.

Kwamitin na sulhu ya yi kira ga bangarorin biyu da su kai hankali nesa. Yayin da shi kuma shugaba Barack Obama na Amirka ya fito fili ya nuna bacin ransa dangane da salon da rikicin na Masar, inda "ya dakatar da atisayen soje na hadin guywa da aka shirya gudanarwa wata mai zuwa."

An dai kafa dokar hana yawon dare a biranen da dama na kasar. Sai dai kuma rahotannin da ke zuwa daga birnin Alkahira sun nunar da cewar magoya bayan Morsi sun banka ma wani ginin gwamnati wuta kusa da babban birnin kasar. Hakazalika sun sha alwashin gudanar da zanga-zanga da suka yi wa lakabi da ta nuna fishinsi bayan sallar jumma'a.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman