Sharif zai miƙa takardar neman tsayawa takara | Labarai | DW | 26.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sharif zai miƙa takardar neman tsayawa takara

Bayan ya koma gida Pakistan daga zaman gudun hijira a waje, a yau ake sa rai tsohon Firaminista Nawaz Sharif zai miƙa takardun neman tsayawa takara a zaɓukan da zasu gudana ƙasa a cikin watan janeru mai zuwa. To sai dai watakila ba zai shiga zaɓen har sai shugaba Pervez Musharraf ya dage dokar ta ɓaci da ya kafa. Sharif wanda Musharraf ya hambarad da gwamnatinsa shekaru takwas da suka wuce, a jiya ya koma gida yana mai cewa zai taimaka a kawo ƙarshen mulkin kama karya a wannan kasa wadda hafsan soji kuma aminin Amirka, wato Musharraf ke yiwa wani bakin mulki bayan kafa dokar ta baci a ranar uku ga wannan wata na nuwamba. A wani labarin kuma rahotanni sun ce a yau gwamnatin Pakistan zata ba da sanarwar ranar da Musharraf zai tuɓe kakin soji.