Shari'ar Tsoffin hukumomin Masar
May 27, 2012Talla
Wata kotu a ƙasar Masar ta yanke wa wani jami'in tsohuwar gwamnatin da aka hambarar daga mulki a cikin watan Maris na shekarar da ta gabata hukuncin ɗaurin shekaru bakwai na zaman gidan jarum bayan da ta same shi da laifin cin hanci.
Zakariya Azumi wanda ke riƙe da matsayin daraktan fadar tsohon shugaban, Hosni Mubarak a lokacin da aka yi juyin juya hali, kotun ta ci shi tara ta kudi dala miliyan shida da dubu 500.
An fara sauraron ƙarar sa ne tun a cikin watan Oktoba,bayan da aka haramta masa ficcewa daga ƙasar, tun cikin watan Maris na shekara ta 2011 makonni ƙaɗan bayan faɗuwar tsohuwar gwamnatin .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh